Dubu Ta Cika: An Cafke Malamin Addini da Ke Satar Yara

Dubu Ta Cika: An Cafke Malamin Addini da Ke Satar Yara

  • Yan sandan Edo sun kama Nicholas Nusa, mai shekaru 50, bisa zargin satar yara mata biyar a karamar hukumar Akoko-Edo
  • Ana zargin Nicholas Nusa wanda ke ikirarin shi malamin addini ne da yi wa daya daga cikin yaran, mai shekaru 15, ciki
  • ’Yan sanda sun ce an kama shi ne bayan samun bayanai, yayin da ake ci gaba da bincike da kokarin mayar da yaran ga iyalansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jjihar Edo - Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wani mai ikirarin malamin addini ne kuma mai kula da Divine Grace Church, Nicholas Nusa, mai shekaru 50, bisa zargin sace yara mata biyar a jihar.

Nicholas Nusa, wanda ke gudanar da cocin a kan titin Imoga da ke Ibillo, karamar hukumar Akoko-Edo, ana kuma zarginsa da yi wa daya daga cikin yaran, mai shekaru 15, ciki.

Kara karanta wannan

Jami'in NDLEA ya nutse yayin farautar mai laifi a cikin kogi

An cafke malamin addini a Edo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yarinyar mai ciki ta haihu ta hanyar fida

Rundunar ’yan sandan ta ce yarinyar da ake zargin Nusa ya yi wa ciki a halin yanzu tana samun kulawar likitoci a wani asibiti, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

An ce an yi mata tiyatar haihuwa, wato Caesarean Section (CS), kuma tana karkashin kulawar kungiyar Brave Heart Organisation.

’Yan sanda sun zargi Nicholas Nusa da sace yaran daga garuruwan Ibillo da Imoga da ke karamar hukumar Akoko-Edo.

An kama shi bayan samun bayanai

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, ta ce Nusa ya amsa zargin da ake masa yayin gudanar da bincike.

Ta bayyana cewa jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne bayan sun samu wasu bayanai da suka kai ga gano shi.

A cewar Eno Ikoedem, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa Nusa ya yi satar yaran biyar ne a lokuta daban-daban tsakanin Satumba 2025 zuwa Afrilu 2026.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga ke hada hadar kudi ta POS, an kama mai taimaka masu

Kakakin rundunar 'yan sandan ta jihar Edo ta bayyana cewa ana zargin ya kai yaran gidansa bayan ya sace su daga kauyukan da suka fito.

Ana kokarin mayar da yaran ga iyalansu

Eno Ikoedem ta ce jami’an tsaro na ci gaba da kokarin hada yaran da iyalansu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ta ce rundunar 'yan sanda za ta ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan zargin da ake yi wa wanda aka kama da kuma tabbatar da yadda lamarin ya faru.

Malamin addini ya shiga hannun 'yan sanda
Taswirar jihar Edo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sandan tafi-da-gidanka, MOPOL, guda huɗu da wasu mutanen kauyen Ayilamo takwas a gundumar Tombo, karamar hukumar Logo ta Benue.

Kauyen Ayilamo da ke kan hanyar Abinsi-Tylen-Anyin-Wukati wanda mutanen cikinsa manoma ne ya sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a lokuta daban-daban.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan shafe sa’o’i ana musayar wuta, ‘yan bindigar sama da 200 sun ja da baya, amma an gano gawarwakin jami’an MOPOL huɗu a cikin jeji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng