Gwamnatin Tinubu Ta Ware Gwamna 1 Ta ba Shi Lambar Yabo saboda Kokarin Tallafawa Mata
- Gwamnatin Tarayya ta karrama gwwmnan jihar Katsina, Dikko Radda saboda kokarin da yake yi wajen tallafa wa mata a jiharsa
- An bai wa gwamnan lambar yabon ne saboda goyon bayansa ga shirin Nigeria for Women Project, wanda aka tsara don agaza wa mata
- Gwamnatin Radda ta bayyana cewa tana kokarin bunkasa tattalin arzikin mata domin taimaka masu su kama sana'ar dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samu lambar yabo ta musamman daga Gwamnatin Tarayya saboda gudunmawarsa wajen bunkasa tattalin arzikin mata a jihar.
An bai wa gwamnan lambar yabon ne a wajen taron majalisar kasa kan harkokin mata, ci gaban yara da bunkasar al’umma karo na 26, wanda aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba, ranar 14 ga Agusta, 2026.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma'a da ta gabata.
Gwamnatin tarayya ta karrama Radda
Sanarwar ta ce an karrama Gwamna Radda ne musamman saboda irin goyon bayan da yake bai wa shirye-shiryen bunkasa tattalin arzikin mata.
Daga cikin manyan abubuwan da suka sa aka yaba wa Dikko Radda shi ne jajircewarsa wajen ganin an aiwatar da shirin Nigeria for Women Project (NFWP).
A sanarwar, ya ce Kwamishinar harkokin mata, Aisha Aminu Malumfashi, ce ta karbi lambar yabon a madadin gwamnan.
Daga bisani ta gabatar da lambar yabon ga gwamnan yayin taron majalisar zartarwar jihar karo na 14 da aka gudanar a jiya a Gidan Gwamnati da ke Katsina.
An yaba da kokarin Radda
An gudanar da taron majalisar kasa ne karkashin taken: “Karfafa iyalai da bunkasa tattalin arziki domin samun ci gaba mai amfani ga kowa: aiwatar da sabon tsarin kare al’umma na Najeriya.”

Kara karanta wannan
An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya
Sanarwar ta ce lambar yabon ta nuna irin kudurin gwamnatin Radda na inganta walwala da hanyoyin samun kudin shiga na mata a fadin Jihar Katsina.
Ta kara da cewa gwamnatin na kokarin fadada damar da mata ke da ita wajen samun tallafin kudi, damar kasuwanci da horar da su kan dabarun sana’o’i domin su samu karfin tattalin arziki da dogaro da kansu.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce:
“Ta hanyar wadannan matakai, gwamnati Radda na karfafa hanyoyin samun abin dogaro ga iyalai tare da samar da damammakin tattalin arziki masu dorewa ga mata."
“Lambar yabon ta kara jaddada kudurin Gwamna Radda na sanya karfafa tattalin arzikin mata cikin manyan ginshikan ci gaba mai amfani ga kowa da kuma gina Jihar Katsina mai karfi, juriya da karfin tattalin arziki.”
Gwamna Radda ya gode wa Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya yi magana kan nadin da aka yi masa a matsayin daraktan yakin neman zaben Shugaba Tinubu na APC a jiihar Katsina.
Radda ya tabbatar wa Shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar APC cewa a shirye yake ya jagoranci yakin neman zabe mai karfi da zai hada kowa a fadin jihar.
Asali: Legit.ng
