Gwamna Ya Dauki Zafi, Ya Aika Sako Mai Zafi ga Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane
- Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo ya gargadi yan bindiga da sauran miyagu su gaggauta tuba ko su bar iyakokin jiharsa
- Ododo ya bayyana cewa gwwmnatinsa ba za ta sassauta ba har sai ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al'umma a fadin jihar Kogi
- Ya ce gwamnatin jihar Kogi na amfani da dabarun yaki da laifuka na soja da kuma wadanda ba na soja ba wajen magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya aika sakon gargadi da yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifiuffuka.
Gwamna Ododo, ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta yakin da take yi da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuffukka ba har sai an kawar da su gaba daya daga jihar Kogi.

Kara karanta wannan
Malamin musulunci ya tsage gaskiya kan batun malamai 500 sun goyi bayan tazarcen Tinubu

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan jiya Juma'a a Kabba, Jihar Kogi, yayin wani gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shi kansa da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC.
Gwamna Ododo ya gargadi yan ta'adda
Gwamna Ododo, wanda mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Commander Jerry Omodare, ya wakilta a wajen gangamin, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba sai ya tabbatar da tsaron al'ummarsa.
Ya bai wa jama'a tabbacin cewa gwamnatin jihar Kogi na amfani da dabarun yaki da laifuka na soja da kuma wadanda ba na soja ba wajen magance matsalar rashin tsaro.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin masu aikata laifuffukan da ke aiki a jihar sun nuna aniyarsu ta mika wuya, sai dai ya jaddada cewa gwamnati ta sanya sakin dukkan mutanen da ke hannunsu a matsayin sharadin amincewa da duk wata yarjejeniyar mika wuya.
An kafa sharadin mika wuya a Kogi
A rahoton Punch, Gwamna Ododo ya ce:
"Dabarunmu na soja da wadanda ba na soja ba suna aiki. Muna fatattakar masu aikata laifuffuka daga kasarmu. Wasu daga cikinsu sun bayyana aniyarsu ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba.
“Amma muna kuma tabbatar masu da cewa dole ne su saki dukkan mutanen da ke hannunsu. Zan iya gaya muku cewa tuni sun fara yin hakan.”

Source: Original
Ododo ya bukaci mazauna mazabar tarayya ta Kabba-Bunu/Ijumu da su ci gaba da mara wa shirye-shiryen gwamnati da manufofinta baya, musamman wadanda suka shafi inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa a fadin jihar.
Yan bindiga sun kashe shugaban APC
A wani rahoton, kun ji cewa miyagun ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi , Hon. Ishaq Yunusa, tarebda yin garkuwa da wani mutum da ke cikin motarsa.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 a kan babbar hanyar Itobe-Ochadamu, kusa da Ojuwo Olijo da ke Karamar Hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Rundunar yan sanda ta ce jami’an tsaro suna binciken dazuzzukan da ke kewaye da wurin domin gano tare da ceto wanda aka yi garkuwa da shi, da kuma cafke wadanda suka kai harin.
Asali: Legit.ng
