‘Yan bindiga sun tare titin Gusau, an nemi wasu fasinjoji da dama a hanya an rasa
- Mahara sun tare hanya a kusa da garin Tsafe tare da sace mutanen da ke cikin motar Sharon da wata tankar mai
- Zargin ya tabata da jama’a suka tabbatar da ganin motocin da aka bar su a buɗe a kan titin Zamfara zuwa Gusau
- Jami'an tsaro sun shiga tsakani sannan suka sake bude hanyar, amma ana tunanin an riga an gama yin barna lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Zamfara - Matafiya da-dama ake tunanin miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da su sakamakon wani hari da aka kai a jihar Zamfara.
A jiya ne ‘yan bindiga suka tare hanyar Gusau zuwa Funtua, a daidai daf da shiga garin Tsafe, karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Source: Getty Images
Harin 'yan bindiga a titin Funtua-Gusau
Wannan lamari da ya faru ranar Juma’a ya tada hankalin matafiya da mutanen yankin Tsafe kamar yadda labari ya zo a jaridar Daily Trust.
‘Yan bindiga sun karbe iko da wannan hanya ta zuwa Gusau mai cike da tsaunuka.
Wani matafiyi da ya sha da kyar a harin ya shaida cewa ‘yan bindigan sun tare titi, suka dauke fasinjojin cikin wata mota kirar Sharon.
Baya ga mutanen da ke cikin karamar motar, an yi gaba da wasu da ke cikin tankar fetur har zuwa yanzu ba a san halin da suke ciki ba.
'Yan bindiga sun bude wuta a kan titi
Matafiyin wanda ya nemi a sakaya sunan shi saboda yanayi na tsaro, ya ce ‘yan bindigan sun dauki lokacin suna ta faman harbe-harbe.
Su ma wasu mazauna garin Tsafe sun yi magana da jaridar, suka ce babu shakka an tare hanya kuma an yi gaba da wasu matafiya.
Wani ya ce:
“Shakka babu mun ji harbe-harbe da kuma karar bindiga sosai. Ya dauki lokaci kafin abubuwa su dawo daidai.”
Sai dai abin da ba su sani ba shi ne adadin mutanen da ‘yan bindigan suka sace.
An ga motoci kan titi babu kowa ciki
Wani bawan Allah da ya wuce bayan harin ya ce ya ci karo da motar sharon da wata motar dauko mai da kofofinta a bude a kan titi.
Yake cewa babu mutum ko daya a cikin motocin amma ga kayan fasinjoji nan a lokacin, haka zalika tankar fetur din na kunne a hanya.

Source: Getty Images
Kokarin da jami'an tsaro suka yi
Lokacin da shi da sauran mutane za su wuce, jami’an tsaro suka share masu hanya har zuwa Tsafe, amma an riga an yi ta’adi kafin nan.
Shi ma ba zai iya cewa ga abin da ya faru da mutanen ba; ko sun tsere cikin daji ne ko kuma ’yan bindigan sun yi garkuwa da su.
An kuma ji cewa akwai wata mota ma da aka gani ta kife a wurin. Duk yunkurin jin ta bakin ‘yan sandan Zamfara bai yi nasara ba.
‘Yan jarida sun tura wa shugaban direbobin tankokin man fetur na reshen Zamfara, Alhaji Shu’aibu Lili, sako amma ba su same shi ba.
Atiku Abubakar zai magance rashin tsaro
A takarar karshe, an ji labari Atiku Abubakar ya sha alwashin maganace matsalar tsaro a shekara daya muddin aka zabe shi a 2027.
‘Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya ce zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya ta hanyar inganta aikin jami'an tsaro.
Atiku Abubakar zai kuma hada-kai da kasashen ECOWAS tare da rage matasa da ke zaman banza.
Asali: Legit.ng


