Lamari Ya Lalace, Yan Bindiga Sun Mamaye Kananan Hukumomi 6 a Jihar Kaduna
- Mutanen kauyuka fiye da 100 sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga a wasu kananan hukumomin Kaduna
- Ana zargin cewa wasu mutane ne ke daukar nauyin hare-haren yan bindigar domin kwace wuraren da ake zaton suna da ma'adanan kasa
- Shugaban ƙungiyar mutanen Kudancin Kaduna, Tabara Kato, ya ce sama da kauyuka 100 ne aka raba da muhallansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa hare-haren yan bindiga sun tilastawa mutanen garuruwa akalla 100 barin gidajensu a wasu kananan hukumomin jihar Kaduna.
Garuruwan da lamarin ya shafa na karkashin kananan hukumomi shida da suka haɗa da Shiroro, Kachia, Kajuru, Kagarko, Chikun da Birnin Gwari.

Source: Original
Yan bindiga sun tashi mutanen kauyuka
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa daga cikin kauyukan da ’yan bindiga suka tarwatsa mutane akwai Aduwa, Ankuro, Akama 1, Gidan Baba Mai Mota, Gidan Yaya, da Gidan Waje.
Sauran sun kunshi Impi Kuturmi, Iriyo, Idebin, Katon Bisa, Kigwali, Kintaro, Kukah, Kurmin Aja, Kurmin Taba, Maigarma, Maraba Barga, Pangyada, Akwana, Tsakiya, Unguwan Alle, Gidan Obere, Dandoka, Tosnin Dodo, Urumo, Takalafiya, Kushinda, Apele da Palapala.
Haka na akwai Ungwan Kuka, Ungwan Pah, Attara, Kurmin Jah, Ankuro, Kurmin Zaki, Ikubiya, Ungwan Lalle, Ungwan Alewa, Dutse, Kigwale, Ariko Village, Ungwan Toka, Baba Maimota, Tsonin Dodo, Gidan Dandoka, Gidan Zamani, Gidan Doigara da Kurmin Taba.
Dubban mutane sun rasa gidajensu
Shugaban ƙungiyar mutanen Kudancin Kaduna, Tabara Kato, ya ce sama da kauyuka 100 ne aka raba da muhallansu, yayin da tsohon kakakin ƙungiyar, Luka Binniyat, ya ce adadin ya kai 245.
Msita Kato ya bayyana cewa jimillar mutane 35,402 ne suka rasa matsugunansu a faɗin jihar.
Hari na baya-bayan nan ya faru ne a ranar 26 ga Yuli a ƙauyen Naridon da ke ƙaramar hukumar Kauru, inda ’yan ta’adda suka kashe aƙalla mazauna ƙauyen 30, ciki har da yara takwas, a wani hari da ya ɗauki tsawon sa’o’i uku.
Da yake magana da wakilin jaridar, Kato ya ce kwace filaye da neman mallakar albarkatun ƙasa ne ke haddasa hare-haren ta’addancin.
Dalilin ruwa wutar ta'addanci a Kaduna
Ya zargi cewa wasu mutane ne ke ɗaukar nauyin maharan da makamai domin korar ’yan asalin yankunan daga filayensu tare da kwace wuraren da ake kyautata zaton suna da arzikin ma’adinai.
A cewarsa, an mamaye wasu garuruwa da dama, inda aka kori mazauna tare da sake wa wasu wuraren suna, sannan baƙin mutane suka mamaye su.
"Ya zuwa yanzu, an tashi mutanen kauyuka fiye da 100, wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa yanzu suna rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira. Suna rayuwa ne cikin tsananin wahala kuma suna fuskantar ƙalubalen yanayi da sauran haɗurra," in ji shi.

Source: Twitter
Kato ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su ƙara zurfafa bincike kan hare-haren domin gano waɗanda ke ɗaukar nauyin tashin hankalin.
Ya kara da cewa kama waɗanda ake zargi ba tare da gano masu ɗaukar nauyinsu ba ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.
“Idan gwamnati da gaske take, za ta iya mayar da hankali kan waɗanda ke ɗaukar nauyin hare-haren.
"Hukumomin tsaro ne suka fi dacewa su gano su ta hanyar gudanar da bincike mai zurfi. Ina fatan gwamnati za ta samu ƙarfin siyasar da za ta bi sahun tushen wannan ta’addanci domin a dawo da zaman lafiya,” in ji Kato.
An yi garkuwa da matar hakimi a Kaduna
Kun ji cewa dakarun Operation 'Enduring Peace' (OPEP) sun kaddamar da aikin ceto da farmaki bayan wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun sace wani likita da matar Hakimi a karamar hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng


