Ban da PFIPC, An Gano Hukumomin Bogi 2 da Adeyemi Ya Kafa kafin a Yi Ram da Shi

Ban da PFIPC, An Gano Hukumomin Bogi 2 da Adeyemi Ya Kafa kafin a Yi Ram da Shi

  • Hukumar ICPC ta gano cewa Adeniyi Adeyemi ya yi amfani da takardun bogi wajen kirkirar wasu hukumomin bogin
  • Wanda ake zargin ya bude asusun bankuna daban-daban da sunayen wadannan hukumomi na FIPA da FIPA-PPP
  • Binciken ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba ta taba kafa hukumomin ko nada Adeyemi ya jagoranci aikinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Prince Adeniyi Adeyemi da ake zargi ya kafa hukumar bogi ta PFIPC ya shiga karin matsala a wajen hukumomi a Najeriya.

Yanzu ake gano cewa baya ga PFIPC, ya yi amfani da takardun karya ya kirkiri wasu hukumomin karya na dabam a gwamnati.

ICPC.
Shugaban hukumar ICPC na kasa, Musa Adamu Aliyu SAN Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Karin hukumomin bogi 2 da aka kafa

Wani kebantaccen rahoton Premium Times ya nuna karin badakalar da ya shiga na bude hukumomi biyu da ba a san da su ba.

Kara karanta wannan

Ana tsoron ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan NYSC 15 a hanyar zuwa Abuja

Jami’an ICPC sun gano cewa ya kirkiro hukumomin bogi biyu masu suna FIPA da FIPA-PPP kuma ya bude masu asusu a banki.

Ya kafa FIPA ne da nufin jawo masu hannun jari a birnin tarayya Abuja, ita FIPA kuma za ta hada kai da ‘yan kasuwa daga waje.

An kirkiro FIPA-PPP da sunan za a hada-kai da ‘yan kasuwa daga ketare domin kawo masu hannun jari su sa kudinsu a Najeriya.

Yadda Adeniyi Adeyemi ya tunkari banki

Shugaban na PFIPC ya tattaro wasu takardu masu dauke da sa-hannun majalisa na karya, ya gabatar a banki domin bude asusu.

Rahoton na musamman ya ce ya bude asusu biyu masu lamba 0059761787 da 0059761718.

Adeyemi ya ratsa cikin gwamnati da takardu da yake nuna wa domin gamsar da jami’ai cewa fadar shugaban kasa ta san da zaman shi.

FIPA da FIPA-PPP sun samu dokokin karya

Rahoton da ICPC ta fitar ya ce tun farko Mista Adeyemi ya kirkiri dokokin da suka kafa FIPA-PPP a karkashin dokokin Najeriya.

Kara karanta wannan

ICPC ta jero sunayen mutane 13 a gwamnati, ta nemi Tinubu ya hukunta su kan kafa hukumar Bogi

A nan ma ya yi amfani da irin takardun da fake da su lokacin kafa PFIPC da PEAC (wanda aka kafa lokacin Muhammadu Buhari).

Da takardun nan ya bude asusu da sunan su a banki amma babu inda Akanta Janar na kasa ya sa hannu yadda dokar kasa ta tanada.

Sunan shugaban PEAC, Adekunle Ajayi da sakatariyarsa aka yi amfani da shi wajen bude asusun a banki ba sa hannun OAFG ba.

Adeyemi shi ne kadai yake iya sa hannu a cire kudi daga asusun wadannan hukumomi.

Adeyemi ya jefa banki da ma'aikata a matsala

Saboda haka ne ICPC ta bukaci a gayyaci duka ma’aikatan bankin da su ka sa hannu a kan bude wannan asusu ba bisa ka’ida ba.

Sauran wadanda za a yi wa tambayoyi su ne Adekunle Ajayi da sakatariyarsa, Lovina Akabueze.

ICPC ta kuma bukaci a duba kudin da ya shigo asusun da kudin da yake ikirarin ya samu ta hanyar karbo wa hukumomin nan bashi.

Badakalarsa ta wuce PFIPC, ya nemi ya kutsa har FEC, ya shiga cikin harkar karbar harajin hatimi da kuma sha’anin ba mutane biza.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: ICPC ta gano sunayen manyan jami'ai 4 da suka taimaka wajen kafa hukumar bogi

Adeyemi ya nemi samun damar karbar kudin shigo da kaya daga ketare har ya nemi ya hada-kai da NOPC, NRS, NIMASA da jami’an NIS.

Majalisa
Ginin Majalisar Tarayya a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abubuwan ban mamaki a badakalar hukumar bogi

Rahoton nan ya yi bayani ne kan abubuwan da suka daure kai game da Prince Adeyemi Adeniyi, wanda ake zargi da kafa hukumar karya.

Duk da zarginsa da amfani da jabun takardu da asusu a CBN, ya bayyana cewa an nada shi ne a bisa ka'ida, yanzu dai ana gaban kotu.

Da bincike ya yi zurfi ne aka fahimci babu halataccen jami’in da ya taba ba Adeyemi mukami kuma ba gwamnati ta kafa hukumar PFIPC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng