ICPC Ta Jero Sunayen Mutane 13 a Gwamnati, Ta Nemi Tinubu Ya Hukunta Su kan Kafa Hukumar Bogi
- Hukumar ICPC ta bukaci a dauki matakin ladabtarwa kan jami’an gwamnati 13 da ake zargi da hannu a badakalar kafa hukumar PFIPC
- Hukumar ta kuma bukaci a gurfanar da Prince Adeniyi Adeyemi kan zargin jabun takardu da kwaikwayon matsayi
- Rahoton binciken ya bayyana yadda PFIPC ta samu damar shiga ofisoshin gwamnati da tsarin hada-hadar kudi duk da cewa ba ta da tushe a doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifuffuka Masu Alaka da Shi ta Najeriya (ICPC) ta ba da shawarar daukar matakin ladabtarwa kan jami’an gwamnati 13.
Hukumar ICPC ta nemi gwamnatin tarayya ta hukunta wadannana jami'ai ne bisa rawar da ake zargin sun taka wajem kafa hukumar bogi ta PFIPC.

Source: Twitter
ICPC ta ba da shawarwari kan PFIPC

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: ICPC ta gano sunayen manyan jami'ai 4 da suka taimaka wajen kafa hukumar bogi
Premium Times ta ruwaito cewa hakan na cikin wani rahoton binciken wucin gadi da ICPC ta gudanar kan yadda hukumar, wadda ba a kafa ta bisa doka ba, ta samu damar shiga ofisoshin gwamnati.
Hukumar ta kuma ba da shawarar gurfanar da Adeniyi Adeyemi, mutumin da ya gabatar da kansa a matsayin Darakta-Janar na PFIPC, bisa zargin kirkirar takardu, kwaikwayon matsayi, bayanan karya da kuma gabatar da bayanan yaudara.
A cikin rahoton wucin gadi da ICPC ta gabatar wa shugaban kasa ranar 6 ga Agusta, 2026, ICPC ta ce gwamnatin tarayya ba ta taba nada Adeyemi ba, sannan PFIPC ba a kafa ta karkashin wata doka.
Jami’ai 13 da ICPC ta ambata
ICPC ta ba da shawarar daukar matakin ladabtarwa kan Mimi Abu, Daraktar Sashen Tsara Kungiyoyi da Ci gaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Sauran sun hada da;
1. Rosemary Achem, mai ba Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya shawara ta musamman kan harkokin gudanarwa.
2. Patricia Akhigbe, mataimakiyar darakta a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa.
3. Aminu Abdullahi, jami’in jadawali a Sashen Rabon Ofisoshi, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya;
4. Bello Abdullahi, mataimakin darakta mai kula da IPSAS da National Chart of Accounts a Sashen Asusun Haɗaka na Ofishin Akanta-Janar na Tarayya
5. Sanni Olubunmi, daraktan Sashen Bincike da Sa-ido na Ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF);
6. Jousha Kadiri Luka, daraktan Sashen Asusun Haɗaka na OAGF.
7. Muazu Balami, mataimakin darakta mai kula da Harkokin Haɗari da Bita a Sashen Bincike da Sa-ido na OAGF;
8. Omameh Florence, mataimakiyar darakta a Sashen Bincike da Sa-ido na OAGF
9. Akinlose Moses, daga Sashen Bincike da Sa-ido na OAGF
10. Ogaba Harry, babban akanta a OAGF
11. Esther Orji Okoli, babbar jami'a a OAGF
12. Ogunbade Habeebat Ajibola, manaja a Sashen Bin Ka’ida da Dokoki na Hukumar Raya Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).

Source: Facebook
Hukumar ICPC ta kuma ba da shawarar cewa hukumomin da lamarin ya shafa su aiwatar da gyare-gyaren da aka gano a cikin rahoton binciken.
Hukumar ICPC ta wanke Gbajabiamila
Kun ji cewa ICPC ta kammala binciken ta game da zargin Femi Gbajabiamila da nadin Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban wata hukumar bogi.
Hukumar ICPC ta ce ba ta gano wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya san da zaman PFIPC ba.
Asali: Legit.ng
