Bayan Faduwar Danyen Mai a Duniya, FCCPC Ta Waiwayo kan Farashin Fetur a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta waiwaiyi farashin da ake sayar da litar fetur a Najeriya bayan saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya
- A halin yanzu, ana sayar da litar fetur kan N1,405 zuwa N1,420 a Abuja, yayin da a Legas take tsakanin N1,325 da N1,370
- Shugaban FCCPC, Tunji Bello, ya ce za a ɗauki mataki kan duk wata dabara ta rashin gaskiya da za ta hana masu saye amfana da raguwar farashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Ƙasa (FCCPC) ta ce tana sa ido sosai kan ci gaba da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Hukumar ta bayyana cewa za ta bibiyi yadda lamarin ke tafiya domin tabbatar da cewa saukin da aka samu a duniya ya haifar da sauƙin kuɗin da ’yan Najeriya ke biya a gidajen mai.

Source: Getty Images
FCCPC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Ondaje Ijagwu, ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2027, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Farashin danyen mai ya sauka
Sanarwar ta ce sun nuna cewa farashin ɗanyen mai na Brent ya ragu daga dala 115 da ya kai a watan Satumba zuwa ƙasa da dala 90 a wannan makon a kasuwannin duniya.
A cewar hukumar, a halin yanzu ana sayar da litar fetur kan farashin da ya kai tsakanin N1,405 zuwa N1,420 a Abuja, yayin da a Legas ake sayar da ita kan N1,325 zuwa N1,370.
FCCPC ta kuma bayyana cewa a ranar 27 ga Fabrairu, kwana ɗaya kafin fara yaƙin da ya shafi Amurka, Isra’ila da Iran, farashin ɗanyen mai na Brent ya kai Dala 72.48 kan kowace ganga.
A wannan lokacin, ana sayar da litar fetur a gidajen mai da ke Legas da Abuja kan farashin da ya kama daga N839 zuwa N925.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi
Dalilin da yan kasuwa ke dogara da shi
FCCPC ta ce ’yan kasuwar man fetur sun sha danganta tashin farashin kayayyakin man fetur a cikin watanni takwas da suka gabata da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai sakamakon rikicin Amurka da Iran.
Shugaban hukumar, Tunji Bello, ya ce ci gaba da raguwar farashin ɗanyen mai zai hana matatun mai da ’yan kasuwa samun kara farashi ko tsayar da shi a matakin da yake.
Bello ya ce hukumar na sa ran raguwar farashin ɗanyen mai za ta haifar da sauƙin kuɗin da ake sayar da fetur ga ’yan kasuwa, sannan a gaggauta mayar da wannan rangwame ga masu saye a gidajen mai.
FCCPC za ta ɗauki mataki
Bello ya ce hukumar na sane da wahalhalun da tsadar fetur ta jefa ’yan Najeriya a ciki tsawon lokaci.
Ya tabbatar da cewa FCCPC za ta ci gaba da bibiyar farashin fetur a kasuwanni, tare da haɗin gwiwar NMDPRA da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da mutne sun samu sauki
NNPC ya tsawaita ragin N66
Kun ji cewa kamfanin NNPCL ya ƙara tsawon mako guda a shirin rangwamen N66 a kowace litar fetur da dizil domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai.
Masu sayen fetur ta hanyar manhajar NNPC za su ci gaba da cin moriyar wannan rangwame har zuwa ranar 14 ga watan Oktoban 2026
Asali: Legit.ng

