Tinubu Ya Yi Kokari kan Kudin Ajiyar Najeriya a Ketare, Ya Kusa na Mulkin Yar’Adua
- Najeriya ta samu karin kudaden ajiyar waje matakin da ya kusa da mafi girman adadin da aka taba samu tun shekarar 2009
- Bayanan Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa ajiyar ta karu da dala biliyan 3.15 tsakanin Yuni da Agusta
- Masana sun ce karin ajiyar zai taimaka wa Najeriya wajen tinkarar matsalolin tattalin arziki daga ketare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ajiyar kudaden waje na Najeriya ta karu zuwa dala biliyan 53.11, wanda shi ne mafi girman matakin da aka samu cikin sama da shekaru 17.
Bayanan Babban Bankin Najeriya, CBN, sun nuna cewa ajiyar ta kai dala biliyan 53.112 a ranar 24 ga Agusta, 2026.

Source: Facebook
Ci gaban da aka samu a Najeriya
Wannan adadi shi ne mafi girma tun ranar 12 ga Janairu, 2009, lokacin da ajiyar kudaden kasar ta kai dala biliyan 53.25, cewar Punch.
Sabon adadin ya bar Najeriya da tazarar dala miliyan 142 kacal kafin ta kai matakin da aka samu a watan Janairun 2009.
Wannan na nuna gagarumin farfadowa a matsayin kudaden ruwa na Najeriya da ake amfani da su wajen mu'amala da kasashen ketare.
An samu saurin karuwar ajiyar tun daga watan Yuni, inda bayanan CBN suka nuna cewa ta tashi daga dala biliyan 49.96 a ranar 3 ga Yuni zuwa dala biliyan 53.11 a ranar 24 ga Agusta.
Wannan ya nuna karin kusan dala biliyan 3.15 cikin wannan lokaci, haka kuma, ajiyar ta karu daga dala biliyan 51.53 a ranar 3 ga Yuli zuwa dala biliyan 53.11 a ranar 24 ga Agusta.
A ranar 27 ga Yuli ne ajiyar ta fara wuce dala biliyan 52, sannan ta kai dala biliyan 52.86 a ranar 21 ga Agusta.

Source: Twitter
Abin da ake tunanin ya haddasa hakan
An danganta ci gaba da tara kudaden ajiyar da karuwar kudaden shiga daga man fetur da kuma karin kwararar daloli cikin tattalin arzikin kasar.
Masana tattalin arziki sun ce karuwar ajiyar ta samar wa Najeriya karin kariya daga matsalolin tattalin arziki da ka iya tasowa daga kasashen waje.
Sun kuma ce hakan na taimakawa wajen inganta kwarin gwiwa a kasuwar musayar kudaden waje, cewar Tribune.
Wannan karin ajiyar na faruwa ne a daidai lokacin da CBN ke aiwatar da tsauraran manufofin hada-hadar kudi, da nufin dakile hauhawar farashi da tabbatar da daidaiton tattalin arziki.
Wani masanin tattalin arziki daga Abuja, Chukwunmonso Iheoma, ya ce: “The rise in reserves strengthens Nigeria’s capacity to manage external pressures and provides greater confidence in the foreign exchange market.”
Ya gargadi hukumomi da su tabbatar da cewa karin ajiyar ya samo asali ne daga dorewar kwararar daloli, ba daga wasu abubuwan wucin gadi ba.
Kudin Najeriya da ke kasashen waje ya ragu
A wani labarin, an ji cewa alkaluman bankin CBN sun bayyana cewa ana samun raguwar kudaden kasar da ke ajiye a asusun kasashen waje.
A watan Mayu, kudin da ya rage a asusun ya ragu da $1.8bn idan aka kwatanta da watan Maris da ake da ragowar $34.44bn a asusun ajiyar wanda yake ta raguwa.
Masana na danganta raguwar da ake samu tun daga watan Fabarairun shekarar nan da biyan basussuka da raguwar fitar da danyen mai.
Asali: Legit.ng

