Yadda Tinubu Ya Yi wa Yar'Adua, Buhari da Sauran Shugabannin Najeriya Fintinkau

Yadda Tinubu Ya Yi wa Yar'Adua, Buhari da Sauran Shugabannin Najeriya Fintinkau

  • Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC, Felix Morka, ya yi magana kan kokarin gwamnatin Bola a Najeriya
  • Morka ya ce Tinubu ya gaji tattalin arzikin da ya lalace, amma sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara dawo da tattalin arzikin Najeriya
  • Ya kuma kare gwamnatin Buhari, yana cewa ta hana Najeriya durƙushewa gaba ɗaya kafin Tinubu ya karɓi mulki a watan Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya yi magana kan salon shugabancin Bola Tinubu.

Morka ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fi dukkan shugabannin Najeriya zaɓaɓɓu da aka yi tun shekarar 1999.

APC ya fadi yadda Tinubu ya fi duka shugabannin Najeriya daga 1999
Asiwaju Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Morka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television, inda ya kare ayyukan gwamnatin Tinubu da manufofinta na tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Bangarorin da Tinubu ya fi sauran shugabanni

A cewarsa, Tinubu ya zarce ayyukan shugabannin da suka gabata, ciki har da Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar’Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.

An tambaye shi abubuwan da ya dogara da su wajen wannan ikirari, sai kakakin APC ya nuna halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki, yana cewa hakan ya isa ya nuna nasarorin gwamnatin.

Ya ce:

"Shugaba Tinubu ya fi sauran shugabannin Najeriya da aka zaba kokari a wa'adinsu na farko.
“Alamomin da ke akwai sun isa su bayyana kansu, kamar yadda muke cewa a fannin shari’a; suna magana da kansu, slwannan shugaban ya gaji tattalin arzikin da ya kasance cikin mummunan hali."

Morka ya danganta matsalolin tattalin arzikin da Tinubu ya gada da kura-kuran gwamnatocin baya, musamman shekaru 16 da jam’iyyar PDP ta shafe tana mulkin tarayya.

Sai dai ya kare gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ta karɓi mulki daga PDP a shekarar 2015, yana cewa gwamnatin Buhari ta taimaka wajen hana Najeriya kara lalacewa kafin Tinubu ya karɓi mulki.

Kara karanta wannan

Da gaske APC ta janye kwamitin kamfen Tinubu na 2027 bayan maganganu?

“Buhari shugaban rikon ƙwarya ne da ya zo ne domin hana ƙasar faɗawa cikin mummunan hali, bayan shekaru 16 na mummunar tafiyar da mulki da gwamnatin PDP ta yi.
“Shugaba Buhari ya yi wa’adinsa, ya kuma yi abin da ya kamata wajen riƙe ƙasar da kyau, domin Shugaba Tinubu ya samu damar karɓar mulki.”
APC ta yabawa salon mulkin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

APC ta kare tsare-tsaren Tinubu

Kakakin APC ya kuma kare sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta gabatar, yana cewa manufofin sun taimaka wajen sake fasalin tattalin arzikin bayan matsalolin da gwamnatin ta gada.

Morka ya ce ana ƙara ganin tasirin sauye-sauyen, har ma a tsakanin wasu mutane da a baya suka soki manufofin gwamnatin.

Ya dage cewa Najeriya ta samu ci gaba a matakin tattalin arziki tun bayan da Tinubu ya hau mulki, yana mai cewa gwamnati ta fitar da ƙasar daga mawuyacin hali.

Kalaman kakakin APC sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da mulki, musamman manufofinta na tattalin arziki da tasirinsu ga ’yan Najeriya.

Tinubu ya yi magana kan ranar Hausa

Kara karanta wannan

"Ka shirya barin Aso Villa"; Melaye ya fadi dabarar ADC ta kifar da Tinubu a 2027

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana Hausawa a matsayin manyan ginshikai da ke taka muhimmiyar rawa wajen hadin kai da ci gaban Najeriya.

Tinubu ya ce harshen Hausa ya bunkasa sosai, inda ya zama daya daga cikin manyan harsunan hadin kai da kasuwanci a duniya.

Shugaban kasar ya taya al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.