Bayan Sace Matasan NYSC, Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Ceto da Dama
- Rundunar ’yan sandan Kogi ta tabbatar da sace wasu ’yan bautar ƙasa da ke tafiya daga Bayelsa zuwa Abuja
- Maharan sun tare motocin bas biyu a hanyar Aloma–Egane, Ofu, inda suka sace wasu fasinjoji, yayin da wasu suka tsere cikin daji
- ’Yan sanda sun ce aikin ceto na ci gaba, yayin da jami’an tsaro ke binciken dazuzzukan yankin domin gano sauran waɗanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Rundunar ’yan sandan Kogi ta tabbatar da sace wasu ’yan bautar ƙasa da ke tafiya daga Bayelsa zuwa Abuja, inda aka samu nasarar ceto mutum 11.
An sace mutanen ne ranar Laraba a kan babban titin Aloma–Egane, cikin ƙaramar hukumar Ofu, bayan wasu ’yan bindiga sun fito daga daji.

Source: Twitter
Yan sanda ta ceto matasan NYSC a Kogi
Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da ceto mutanen ne ranar Juma’a, bayan da wakilin jaridar ya tuntube ta domin neman ƙarin bayani kan lamarin, cewar Punch.
Yan bindiga sun tare motocin bas biyu da ke tafiya a saɓanin juna, kafin su yi awon gaba da wasu fasinjoji, yayin da wasu suka tsere.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Salisu Oyiza Afusat, ta ce jami’in ’yan sanda na Ofu ya jagoranci haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa wurin.
Ta ce hakan ya biyo bayan samun kiran gaggawa daga mutanen da suka gano harin, inda jami’an tsaro suka fara ɗaukar matakan ceto cikin gaggawa.
An gano motocin da aka bari, ciki har da wata farar motar Peace Mass Transit Hummer da kuma motar bas mai kujeru 18, cewar jaridar FIJ.
A cewar Afusat, aikin haɗin gwiwar jami’an tsaro ya haifar da nasarar ceto mutum 11 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, ciki har da direbobin motocin bas ɗin biyu.
Ta ce:
"Mun gano cewa mafi yawan wadanda aka ceto din matasa ne masu bautar kasa da suke tafiya daga Bayelsa zuwa Abuja."

Source: Original
Ta ƙara da cewa an yi wa mutanen da aka ceto tambayoyi domin samun bayanai kan abin da ya faru, kafin a bar su su ci gaba da tafiyarsu.
Afusat ta ce aikin jami’an tsaro na ci gaba a dazuzzukan da ke kewaye da wurin, musamman domin ceto sauran waɗanda ake zargin suna hannun masu garkuwa.
Ta ce wani babban burin jami’an tsaron shi ne gano tare da kama waɗanda suka shirya harin, domin gurfanar da su gaban kotu bisa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa tana amfani da dukkanin kayan aiki da bayanan sirri da take da su domin tabbatar da tsaron yankin.
Ta kuma ce jami’an tsaro za su ci gaba da ƙoƙarin gano duk wasu mutanen da suka rage a hannun masu garkuwa da su.
Wannan tabbacin ’yan sandan ya zo ne bayan wata mata da ta bayyana kanta a matsayin ’yar’uwar ɗaya daga cikin ’yan bautar ƙasar ta roƙi gwamnati ta shiga tsakani.
Tinubu ya kawo sababbin tsare-tsare a NYSC
Mun ba ku labarin cewa bayan tsawon lokaci ministocin Najeriya ba za su yi zama domin taron FEC, an yi ganawar a fadar Aso Rock a Abuja.
Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da wasu manyan gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima da aka fi sani da NYSC.
Sauyin da aka samu zai taimaka wajen taimaka wa matasa, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma kiyaye rayuka.
Asali: Legit.ng


