Jerin Gyare Gyare 7 da Gwamnatin Tinubu Ta Yi wa NYSC a Karon Farko tun 1973

Jerin Gyare Gyare 7 da Gwamnatin Tinubu Ta Yi wa NYSC a Karon Farko tun 1973

  • Bayan tsawon lokaci ministocin Najeriya ba za su yi zama domin taron FEC, a ranar Litinin an yi ganawar a fadar Aso Rock a Abuja
  • Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da wasu manyan gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima da aka fi sani da NYSC
  • Sauyin da aka samu zai taimaka wajen taimaka wa matasa, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma kiyaye rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi wa tsarin bautar kasa na NYSC wani babban garambawul bayan shekara da shekaru da kirkiro shi.

An samu wannan gagarumin sauyi ne bayan amincewar Majalisar zartarwa ta tarayya a wani zama da aka yi a Fadar Aso Rock a Abuja.

NYSC.
Shugaba Bola Tinubu yana sa hannu a takarda da hoton wata yar NYSC mai yi wa kasa hidima Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan matasa ya sanar da sauyi a NYSC

Ministan harkokin matasa ya yi dogon bayani a shafinsa na X dauke da jerin canje-canjen da aka amince a yi wa tsarin yi wa kasa hidima.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya

Ayodele Olawande mai kula da harkokin cigaban matasa a Najeriya ya ce wannan gyara shi ne irin shi na farko tun kafa NYSC a 1973.

Mista Ayodele Olawande ya ce manufar hakan ita ce a ba matasa kwarewa da kuma damammakin da suke bukata ganin yadda duniya ta canza.

Ministan ya kuma ce wannan yana cikin hangen nesan shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganin karfin tattalin arzikin Najeriya ya kai $1tr.

Yar NYSC mai yi wa kasa hidima
Wata yar NYSC dauke da akwatin ta a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun 2025 aka fara aikin canza tsarin NYSC

Sanarwar Ministan harkokin matasan ta ce tun a shekarar 2025 aka fara wannan yunkuri a karkashin ma’aikatarsa da kuma ta ilmi.

Haka zalika Mai taimaka wa shugaban kasa wajen manufofin gwamnati ta bada gudumuwarta kafin canjin ya samu amincewr FEC a yau.

Punch ta rahoto cewa Majalisar ministocin na FEC sun amince a sauya NYSC ta yadda wadanda suka gama karatun za su koyi aiki da kyau.

Wani canjin da za a gani shi ne, sjoji za su daina rike shugabancin hukumar kamar yadda a baya aka san kujerar DG da Birgediya Janar.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi

Sauye-sauyen da aka yi wa NYSC

  1. Tsarin tura matasa garuruwan bauta da ya dogara da fasaha
  2. La’akari da barazanar tsaro wajen tura matasa domin kare masu yi wa kasa hidima
  3. Sabon tsarin zama a sansanin NYSC na tsawon makonni shida da zai maida hankali wajen koyar da harkar shugabanci, kasuwanci, ilmin fasahar zamani
  4. Amfani da kwarewa wajen tura jama’a wurin aiki daidai da ilmin da aka karanta da kuma tafarkin aiki.
  5. Shugabanci na zamani a tsarin mulkin farar hula yayin da sojoji za su cigaba gudunmuwar tsaro
  6. Inganta sansanin bautar kasa ta hanyar kawo tsarin tantancewa da auna tsarin a fadin kasa.
  7. Sabon tsarin biki da zai canji shirin yaye matasa da kuma khaki da aka sabunta wadanda za su yi daidai da sanin aiki da kishin kasa

Ana so a hana Bola Tinubu takara

Rahoto ya zo a makon nan cewa kungiyar CFRPA ta sake taso da batun ingancin shaidar digirin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na jami'ar Amurka.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Kungiyar ta CFRPA tana da ta-cewa game da sauran takardun karatunsa shugaban kasar don haka ta bukaci a hana shi tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Tinubu wanda tuni ya samu tikitin sake neman takarar shugaban kasa a APC ya tsallake duk wasu shari'a a zaben farko da ya tsaya a farkon 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng