Hisbah Ta Kama Amarya da Ango kan Daura Aure a Sadaki N10,000 ba Sanin Iyaye a Kano
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin yin aure ba tare da amincewar iyaye ba
- Rahoto ya ce cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango, da wasu uku da suka shiga wajen shaidar aure
- Hisbah ta byyana cewa an yi auren ne da sadaki na ₦10,000 wanda bai kai ka’idar da Musulunci ya tanada ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyar bisa zargin shirya aure ba bisa ka’ida ba tare da samun amincewar iyayen amarya ba.
Rahoton ya bayyana cewa an kulla auren ne da sadakin da ya yi kasa da kima, abin da ya sabawa tsarin Musulunci da doka.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa mataimakin shugaban hukumar, Dr Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hisbah ta kama amarya da ango a Kano
Dr Mujahideen Aminuddeen ya ce wadanda aka kama sun hada da amarya, ango da wasu mutum uku da suka shiga cikin shirin a matsayin shaidu da wakilai.
Aminuddeen ya kara da cewa hukumar ta fara bincike don gano cikakken abin da ya faru da kuma dalilan da suka sa matasan suka yi auren ba tare da bin ka’idar da doka ta tanada ba.
Hukuncin aure ba tare da izinin iyaye ba
Dr. Aminuddeen ya bayyana cewa wannan aure ya sabawa tsarin Musulunci wanda ke bukatar samun izinin iyayen amarya kafin a kulla aure.
Ya kuma shawarci iyaye da su kula da harkokin ‘ya’yansu, musamman a al’amuran da suka shafi aure, domin gujewa irin wadannan matsaloli da ke iya janyo rikici da keta dokokin addini.

Source: Facebook
An daura aure a kan sadakin N10,000
Rahoton ya ce sadakin da aka yi amfani da shi a wannan aure ya kasance ₦10,000, wanda bai kai matakin da Musulunci ke dauka a matsayin sadaki ba.
Vanguard ta wallafa cewa hukumar Hisbah ta bayyana cewa hakan ya nuna rashin bin tsari da rashin girmama dokokin addinin Musulunci.
A mazhbar Malikiyyah da ake amfani da shi a Najeriya, ana yanek mafi karancin sadaki.
Fadakarwa daga Sheikh Al-Juzuri
A tattaunawa da Legit Hausa, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya bayyana cewa auren mace ba tare da izinin waliyyinta ba, ba shi da inganci bisa tsarin Musulunci.
Malamin ya ce:
"Malaman mazhabar Malikiyya sun yi ittifaki cewa dole ne mace ta samu amincewar waliyyi kafin a yi mata aure, bisa ga hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce: “Babu aure sai da waliyyi.”"
Ana shirin auren gata a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano na shirin gudanar da auren gata na ma’aurata 2,000.
Bayanai da Legit ta samu sun nuna cewa za a yi bikin ne domin saukaka aure da karfafa tsabtatacciyar rayuwa a tsakanin matasa a jihar.
A halin yanzu dai jama'ar jihar na jiran karin haske daga gwamnatin Kano da hukumar Hisbah kan yadda bikin zai gudana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

