An Tafka Babban Rashi: Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An shiga jimami a jihar Oyo bayan sanar da rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin jihar wanda ya tayar da hankula
- Marigayin ya rike mukamin SSG a lokacin mulkin marigayi tsohon Gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi, kafin rasuwarsa
- Iyalansa sun sanar da rasuwarsa, inda suka bayyana shi a matsayin uba, miji, kakansu, dan’uwa kuma suka nemi addu’o’i da goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Iyalan tsohon Sakataren Gwamnatin Oyo, Alhaji Abdul Waheed Akintola Olajide sun tabbatar da rasuwarsa a jihar wanda ya ba da gudummawa sosai.
Rahotanni sun bayyana cewa Olajide, wanda ya rike mukamin SSG a gwamnatin marigayi tsohon Gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi, ya rasu ranar Talata.

Source: Original
Iyalansa ne suka sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, inda suka bayyana shi a matsayin ƙaunataccen miji, cewar The Guardian.
Sakataren gwamnatin Ondo ya bar duniya
A kwanan nan ma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani tsohon sakataren gwamnatin jiha ya yi bankwana da duniya a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Sakataren Gwamnatin jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye ya yi bankwana da duniya bayan fama da raunin haɗarin mota.
An nada Oluseye a matsayin SSG a ranar 24 ga Janairu, 2024, kuma ya yi hidima da kwazo da jajircewa ga jiharsa har zuwa mutuwarsa.
Mutuwarsa ta girgiza al'ummar jihar Ondo da Akure, inda mutane da dama ke alhini da jimami kan rashin shugaba mai kishin jama’a.

Source: Facebook
Bukatar iyalan marigayin ga al'ummar jihar
Sun kuma bayyana marigayin a matsayin uba, kaka, kawu, ɗan’uwa da kuma dan uwa na kusa, tare da gode wa Allah saboda rayuwarsa da kuma gudummawar da ya ba al'umma.
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Cike da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa rayuwar da ya yi mai albarka, tare da mika wuya ga hukuncinsa, muna sanar da rasuwar ƙaunataccen mijinmu, mahaifinmu, kakanninmu, kawunmu, ɗan’uwanmu da ɗan uwanmu, Alhaji Abdul Waheed Akintola Olajide, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a yau, 25 ga Agusta, 2026.
"Allah Ya bai wa iyalansa baki ɗaya da dukkan masoyansa ƙarfi, haƙuri da kwanciyar hankali domin jure wannan babban rashi."
Iyalin sun nemi jama’a da su yi musu addu’a tare da ba su goyon baya yayin da suke jimamin rasuwar mamacin.
An shirya gudanar da sallar jana’izar marigayin da ƙarfe 11:00 na safe ranar Laraba a MAN Centre, Oke Ado, Ibadan, kamar yadda Daily Post ta ce.
Tsohon SSG a Kwara ta rasu
A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga jimami a jihar Kwara bayan samun labarin rasuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Saka Abimbola Isau.
Marigayin wanda ya taɓa riƙe muƙamin Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kwara, ya rasu bayan ƴar gajeruwar jinya a ranar Asabar, 4 ga Janairun 2026.
Gwamnan Kwara, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq ya aika da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin wanda ya taka rawa a fagen siyasar jihar.
Asali: Legit.ng

