Hisbah ta kama wasu ma’aurata a kan yin aure ba tare da izinin iyayensu ba a Kano

Hisbah ta kama wasu ma’aurata a kan yin aure ba tare da izinin iyayensu ba a Kano

Jami’an Hukumar daidaita tarbiyya da dabbaka shariar Musulunci a jahar Kano, Hisbah, ta kama wasu masoya biyu da suka yi gaban kansu wajen daura ma kansu aure ba tare da izini ko sahhalewar iyayensu ba.

Rahoton jaridar Labarai24 ta bayyana cewa masoyan biyu wanda dukkansu mazaun unguwar Kurna a cikin garin Kano, sun dauki matakin auren junansu ne baya n sun ido biyu da wani mutumi da matarsa suna rungumar juna a bainar jama’a yayin da suke tafiya a kan hanya.

KU KARANTA: Malam El-Rufai ne kadai ke da hurumin sakin Sheikh Zakzaky – gwamnatin tarayya

Daga nan ne masoyan suka gayyaci abokansu domin su zamto waliyyansu, kuma suka daura ma kansu aure a kan kudi N20,000, kamar yadda mataimakin kwamandan Hisbah, Malam Shehu Tasiu Ishaq ya bayyana.

A wani lamari mai ban dariya da ban haushi, kwamandan yace da yake saurayin bas hi da kudi, N2,000 kacal yake dasu a hannunsa, sai budurwar da aka sakaya sunanta ta ranta ma cikon N18,000, a haka sadakin aure ya cika dubu 20 cif cif.

Malam Shehu Ishaq ya kara da cewa bayan watanni uku da wannan aure, sai matar ta samu ciki, amma yace ba za’a kira zaman da masoyan biyu suka yi da zaman zina ba, kuma abin dake cikin matar bad an shege bane.

Daga karshe, Malam Shehu ya yi kira ga ma’aurata da su kiyayi rungumar juna a bainar jama’a, domin kuwa hakan na na haifar da rashin ɗa’a a cikin al’umma.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ogun sun sanar da kama wani magidanci dan shekara 37, Mutiu Sonola a kan lafin lakada ma matarsa, Zainab dan banzan duka da ya yi sanadiyyar mutuwarta har lahira.

Mai magana da yawun Yansandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, inda yace sun kama Mutiu a ranar Laraba ne bayan mahaifinta ya kai musu rahoton lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel