Babban Malamin Musulunci, Sheikh Anchau Ya Rasu, Jingir Ya Masa Jana'iza

Babban Malamin Musulunci, Sheikh Anchau Ya Rasu, Jingir Ya Masa Jana'iza

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Malam Muhammadu Anchau, ya rasu bayan ya shafe lokaci yana fama da jinya a garin Jos na jihar Plateau
  • Sheikh Sani Yahaya Jingir ya jagoranci gudanar da sallar jana'izar marigayin, wanda rasuwarsa ta girgiza al'ummar Musulmi da malaman addini
  • Mutane da dama sun bayyana alhininsu tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa Malam Anchau, Ya jikansa tare da sanya Aljanna ta zama makomarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jos, Plateau - An shiga jimami bayan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Malam Muhammadu Anchau, wanda ya rasu bayan doguwar jinya a garin Jos.

Rasuwar malamin ta jefa almajiransa, sauran malaman addini da al'ummar Musulmi cikin alhini, yayin da aka gudanar da sallar jana'izarsa a garin Jos.

Kara karanta wannan

Za a cigaba da shagalin Mauludi a Kano, Abba ya ba da hutun takutaha

Jana'izar Sheikh Muhammadu Anchau
Marigayi Sheikh Muhammadu Anchau. Hoto: Sa'id Mansur Sa'id
Source: Facebook

Bayanin da Sa'id Mansur Sa'id ya wallafa a Facebook ya nuna cewa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya halarci jana'izar tare da jagorantar yi wa marigayin sallah.

Sheikh Jingir ya yi jana'iza

An bayyana cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya jagoranci sallar jana'izar marigayi Malam Muhammadu Anchau, wanda Allah Ya yi wa cikawa bayan doguwar jinya.

Haka kuma, bayanai sun nuna cewa Malam Anchau ya yi hulɗa da manyan malaman addinin Musulunci da dama a tsawon rayuwarsa.

Daga cikin malaman da aka ambata cewa yana da alaƙa da su akwai Sheikh Isma'ila Idris da Malam Adamu Ibrahim Mai-Shafi.

An bayyana Malam Anchau a matsayin malamin da ya ba da gudunmawa wajen koyar da ilimi da kuma taimaka wa al'umma.

An yi wa Malam Anchau addu'a

Bayan yaɗuwar labarin rasuwar malamin, mutane da dama sun bayyana alhininsu tare da yin addu'ar Allah Ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

Sanata Barau yi fito da me Sheikh Jingir ke nufi da Muslim Muslim

Wasu daga cikin masu yin addu'ar sun bayyana cewa Allah Ya karɓi bakuncinsa, Ya gafarta masa zunubansa tare da sanya Aljanna ta zama makomarsa.

Haka kuma, an yi addu'ar Allah Ya sanya jinyar da ya yi ta zama kaffara a gare shi, tare da yi wa iyalansa da almajiransa addu'ar samun haƙuri.

Jana'izar Sheikh Muhammadu Anchau
Wajen jana'izar Sheikh Muhammadu Anchau. Hoto: Said Mansur Sa'id
Source: Facebook

Mutane da dama sun bayyana cewa Malam Muhammadu Anchau ya bar kyakkyawan tarihi saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen koyar da ilimin addinin Musulunci.

An roki Allah Madaukakin Sarki Ya jiƙan Malam Muhammadu Anchau, Ya gafarta masa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa tare da sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.

Wanda ya kashe Musulmai ya mutu

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa tsohon kwamandan sojojin Sabiya na Bosnia, Ratko Mladic, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Ratko Mladic ya rasu yana zaman daurin rai da rai a wani gidan yari na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Hague saboda laifukan kisan kare dangi da laifukan yaki.

An yanke masa hukuncin daurin rai da rai a shekarar 2017, sannan kotun Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da hukuncin bayan daukaka kara a shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng