Karshen Alewa: Sojan da Ya Kashe Dubban Musulman Kasar Bosnia Ya Mutu
- Tsohon janar na Bosniya dan kabilar Serb, Ratko Mladic, ya mutu yana da shekaru 84 yayin da yake zaman daurin rai da rai
- An same shi da laifin kisan kare dangi, laifukan yaki da cin zarafin bil'adama kan abubuwan da suka faru a yakin Bosnia
- Ya jagoranci sojojin Bosniya Serb a yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100,000 ciki har da tarin Musulmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Netherlands – Tsohon janar na Bosniya dan kabilar Serb da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan kisan kare dangi da laifukan yaki, Ratko Mladic ya mutu yana da shekaru 84.
Mladic ya mutu ne a wani asibitin gidan yari na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin The Hague na kasar Netherlands, kamar yadda kotun kasa da kasa ta tabbatar a ranar Alhamis.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa alkalin kotun, Graciela Gatti Santana, ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan halin da ya kai ga mutuwar tsohon janar din.
An kama Mladic da laifin yaki
AP ta rahoto cewa an yanke wa Mladic hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin shirya kisan kiyashi a Srebrenica a shekarar 1995.
A kalla maza da samarin Bosniak, wato Musulman Bosniya, 8,000 ne aka kashe a yankin da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin wurin da ya kamata jama'a su samu kariya.
Kotun kasa da kasa ta bayyana laifukan da aka same shi da aikatawa a matsayin wasu daga cikin mafi muni da aka taba aikatawa a kan bil'adama.
An yanke masa hukunci a shekarar 2017 kan laifukan kisan kare dangi, laifukan yaki da kuma cin zarafin bil'adama da suka faru tsakanin shekarun 1992 zuwa 1995.
Me Mladic ya aikata a Bosnia?

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke wa babban malamin addinin musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai, ta fadi laifinsa
Lokacin da yakin Bosnia ya barke a shekarar 1992, Mladic ya zama kwamandan sojojin Bosniya Serb, inda ya jagoranci mamaye yankuna masu yawa.
A karkashin jagorancinsa, sojojin Serb sun yi wa birnin Sarajevo kawanya tare da kai hare-hare kan wasu garuruwa da kauyuka.
An kuma kafa wuraren tsare fursunoni tare da kashe mutane da dama, yayin da rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100,000 tare da tilasta wa sama da mutane miliyan 2 barin gidajensu.
Batun kashe dubban Musulmai
Kisan kiyashin Srebrenica ya faru ne a watan Yulin 1995, inda aka kashe dubban maza da samarin Musulman Bosniya cikin kwanaki kadan.

Source: Getty Images
An birne gawarwakin mutane da dama a kaburburan gama-gari, yayin da daga baya aka kwashe wasu zuwa wasu wurare domin boye shaidun abin da ya faru.
Kotun kasa da kasa ta ce manufar yakin ita ce korar Musulman Bosniya, 'yan Croatia da sauran wadanda ba 'yan kabilar Serb ba daga wasu yankunan kasar.
Mladic ya kasance cikin mutanen da aka danganta da wani shirin aikata laifuka tare da tsohon shugaban Serbia, Slobodan Milosevic da tsohon shugaban Bosniya Serb, Radovan Karadzic.
CIA ta gargadi Rasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban hukumar leken asirin Amurka ta CIA, John Ratcliffe, ya kai wata ziyarar sirri zuwa birnin Moscow na kasar Rasha.
Rahotanni sun ce Ratcliffe ya gargadi gwamnatin shugaban Rasha, Vladimir Putin, kan kai hari wani yanki na kungiyar tsaro ta NATO.
An ce jami'an Amurka da na Turai suna fargabar cewa Rasha na iya gwada karfin kungiyar NATO ta hanyar kai wani takaitaccen hari.
Asali: Legit.ng

