Duniya Labari: Babban Malamin Musulunci kuma Shugaban JIBWIS Ya Rasu

Duniya Labari: Babban Malamin Musulunci kuma Shugaban JIBWIS Ya Rasu

  • An tabbatar da rasuwar wani shugaban kungiyar Izala ta JIBWIS reshen birnin Makurdi da ke jihar Benue a Tsakiyar Najeriya
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa Muhammad Nasir Musa Gwani ya rasu a karshen mako, lamarin da ya jefa al’ummar Musulmi cikin jimami
  • Sakataren kungiyar Sunnah Youths Association, Yusuf Magaji, ne ya sanar da rasuwar malamin, inda ya bayyana kokarinsa ga addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Makurdi na Benue, ya rasu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa malamin mai suna Muhammad Nasir Musa Gwani ya riga mu gidan gaskiya a karshen mako.

Malamin Musulunci ya rasu a Benue
Shugaban kungiyar JIBWIS a Makurdi, Muhammad Nasir Musa Gwani ya rasu. Hoto: Yusuf M Magaji.
Source: Facebook

Wani matashi mai kokarin ba da gudunmawa a addinin Musulunci, Yusuf M Magaji shi ya bayyana rasuwarsa limamin a shafin Facebook.

An bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba, yayin da al’ummar Musulmi ke jimamin mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin Maulidin Annabi Muhammad SAW

JIBWIS da aka fi sani da Kungiyar Izala, babbar kungiyar Musulunci ce ta Ahlus-Sunnah da aka kafa a Najeriya a shekarar 1978.

An kafa kungiyar ne domin inganta koyarwa da ayyukan Musulunci bisa Alkur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (S.A.W).

Mutuwar Imam Muhammad Nasir ta jawo matukar bakin ciki tsakanin al’ummomin Musulmi a Benue da sauran wuraren da aka san shi.

Yusuf Mohammed Magaji, sakataren kungiyar Sunnah Youths Association, reshen North Bank, ne ya sanar da rasuwar a safiyar Lahadi, 23 ga Agusta.

Magaji ya sanar da rasuwar ne ta wata sanarwa da ya sanya hannu tare da wallafa ta a shafinsa na Facebook.

Ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen malamin addinin Musulunci wanda rayuwarsa gaba daya ta kasance wajen koyar da Musulmi ilimin addini.

Magaji ya ce:

“Mun wayi gari a yau da wani labari mai matukar bakin ciki na rasuwar masoyinmu Imam Muhammad Nasir Musa Gwani, shugaban JIBWIS Makurdi.”

A cikin sakon ta’aziyyarsa, Magaji ya bayyana cewa duniyar Musulunci ta rasa wani mutum da rayuwarsa ta kasance gaba daya wajen yada ilimin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Musulmi sun yi rashi a Arewa, babban limami ya riga mu gidan gaskiya

Ya ce marigayin ya shafe rayuwarsa yana koyar da al’ummar Annabi Muhammad (S.A.W.) ilimin addini ba dare ba rana.

Kungiyar Sunnah Youths Association ta nada Imam Muhammad Nasir a matsayin uban kungiyar watanni uku kacal kafin rasuwarsa, lamarin da ya kara jefa mambobinta cikin bakin ciki.

Kungiyar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, JIBWIS Makurdi, JIBWIS Benue, JIBWIS Najeriya da daukacin Musulmi a duniya.

Magaji ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

A baya, an ruwaito rasuwar Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Saliu, wanda ya rasu bayan shekaru masu yawa yana hidimtawa Musulunci.

Babban sakataren malamin, Abdulazeez Arowona, ne ya tabbatar da rasuwar Sheikh Saliu, wanda ya shahara wajen hidimtawa Musulunci da masarautar Ilorin.

Malamin Musulunci, Sheikh Kamal ya rasu

Mun ba ku labarin cewa al’ummar Musulmi a Alfeti a Ankpa ta sanar da rasuwar Sheikh Mustapha Kamal Ahmad, babban limamin garin.

Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci da jagorantar al’umma, yayin da dalibai da mabiyansa ke yi masa addu'a.

Sanusi Abdul Sanusi ya bayyana rasuwar Sheikh Ahmad a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Musulmi da yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.