Kaico: Ɗa Ya Kashe Mahaifinsa Shugaban APC a Wani Yanayi Mai Tada Hankali

Kaico: Ɗa Ya Kashe Mahaifinsa Shugaban APC a Wani Yanayi Mai Tada Hankali

  • Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan wani shugaban APC na mazaba, Julius Bello, wanda aka fi sani da De Lord Ogata
  • Ana zargin ɗansa mai suna Irobudo ya yi amfani da guduma mai nauyi wajen bugun kansa har ya mutu
  • Majiyoyin daga cikin iyalinsa sun ce ɗan ya kashe mahaifinsa ne saboda zargin da yake cewa shi ne sanadin talaucinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan wani jigon jam’iyyar APC mai mulki, Julius Bello, wanda aka fi sani da De Lord Ogata.

Bayanai sun nuna cewa ana zargin ɗansa mai suna Irobudo ne ya kashe shi a Fugar, ƙaramar hukumar Etsako Central ta jihar Edo.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa wanda ake zargin ya yi amfani da guduma mai nauyi wajen bugun mahaifinsa a kai.

Kara karanta wannan

"Adadin mutanen da suka sayi hannun jari a matatar Dangote ba su kai yadda aka so ba"

Rahotanni sun ce matashin ya tsere, kuma har yanzu yana can yana buya, yayin da ’yan sanda suka fara bincike kan lamarin. Kisan ya jefa iyalin mamacin da al’ummar Fugar cikin jimami da mamaki.

Abin da ya tada hankalin mutane

Yanayin da ya kai ga faruwar lamarin ya kuma haifar da tambayoyi masu tayar da hankali sakamakon zargin da aka yi cewa malamai masu ikirarin ana masu wahayi ne suka yi tasiri a zuciyar matshin.

Bello, wanda shi ne shugaban APC na mazaba ta uku a Fugar, an ruwaito cewa an kai masa hari tare da kashe shi ranar Lahadi, jim kaɗan bayan ɗansa ya dawo daga Legas a ƙarshen mako.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana zargin matashin ya juya wa mahaifinsa baya ne bayan wasu malamai sun gaya masa cewa Bello ne sanadin ci gaba da talaucinsa da kuma rashin samun nasara a rayuwarsa.

Yadda da ya kashe mahaifinsa a Edo

Kara karanta wannan

An yi hasashen ranar da za a yi tashin duniya a 2026 da muke ciki

Ana kyautata zaton waɗannan zarge-zarge, waɗanda suka jefa shi cikin shakku da ƙiyayya ga mahaifinsa, sun taka rawa kafin mummunan rikicin da ya faru tsakaninsu.

Abin da ya kamata ya zama tarbar farin ciki tsakanin uba da ɗansa bayan dawowar matashin daga Legas, a cewar rahoton, ya rikide zuwa mummunan lamari, wanda ya bar iyalin cikin alhinin rashin shugaban su da kuma yanayin mutuwarsa.

Mamacin, wanda fitaccen ɗan siyasa ne a mazabarsa, an ruwaito cewa an kai masa hari ta hanyar da ta jawo masa munanan raunuka a kai har suka yi sanadin mutuwarsa.

’Yan sanda sun fara bincike

Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Edo, Eno Ikoedem, ta ce an kai rahoton kisan ga ’yan sanda kuma sun fara bincike.

Ta ƙara da cewa wanda ake zargin ya gudu, yayin da rundunar ke ƙoƙarin gano yadda lamarin ya faru da kuma cafke shi.

Ana sa ran binciken ’yan sanda zai gano dalilin harin tare da fayyace jerin abubuwan da suka kai ga mutuwar wannan jigon APC.

Saurayi ya kashe budurwarsa a Edo

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi

Kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Edo ta kama wani matashi mai suna Miracle Samuel, mai shekara 21, bisa zargin kashe budurwarsa wadda ya haɗu da ita a kafar sada zumunta.

Kwamishinan ’yan sanda ya ce wanda ake zargin ya gayyaci budurwar zuwa gidansa da ke yankin Ahor a Benin City, inda ake zargin ya kashe ta da wuƙa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262