Gwamna Uba Sani Ya Kinkimo Basussuka tun bayan Hawa Mulki? An Ji Gaskiyar Zance
- Gwamna Uba Sani ya ce bai ciwo ko sisi na sabon bashi ba tun lokacin da ya zama gwamnan Kaduna.
- Gwamnatin Kaduna na kashe kusan Naira biliyan 6.7 a kowane wata wajen biyan bashin da gwamnatocin baya suka karbo
- Uba Sani ya ce an gano yara kusan 550,000 da ba sa zuwa makaranta, yayin da sama da 300,000 daga cikinsu aka mayar da su makarantu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta karɓi sabon bashi ko sisi ba tun bayan da ya hau kujerar gwamna a shekarar 2023.
Gwamna Uba Sani ya bayyana bai karbo bashi ba duk da cewa gwamnatinsa tana ci gaba da biyan basussukan da gwamnatocin baya suka karbo.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today.
Kaduna na biyan Naira biliyan 6.7 duk wata
Gwamna Uba Sani ya ce jihar Kaduna na biyan kusan Naira biliyan 6.7 a duk wata domin hidimar basussukan da aka gada daga gwamnatocin baya.
Ya ce, duk da wannan nauyi, ya yanke shawarar cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara karɓar bashi ba.
“Tun da na zama gwamna, ban ciwo ko sisi na bashi ba,” in ji Uba Sani.
Ya danganta wannan matsaya da yadda gwamnatinsa ke gudanar da kuɗaɗen jihar cikin tsari, tare da fifita muhimman ayyukan da ya ce za su amfani al’umma.
“Abin ya shafi taka-tsantsan wajen kashe kuɗi. Ya shafi zaɓar inda za a saka kuɗin da kuma yin taka-tsantsan wajen zuba jarin,” in ji shi.
Uba Sani ya jero nasarorin gwamnatinsa
Gwamnan ya kuma bayyana gwamnatinsa a matsayin mai samun nasara, yana mai cewa ta samu ci gaba a fannoni da suka haɗa da noma, ilimi, samar da ababen more rayuwa, koyar da sana’o’i da kuma tsaro.
Ya ce gwamnatinsa na amfani da bayanan da aka tattara domin gano matsalolin da ke addabar al’umma da kuma tsara hanyoyin magance su yadda ya kamata.
An gano yara 550,000 ba sa zuwa makaranta
A bangaren ilimi, Uba Sani ya bayyana cewa jihar ta gano kusan yara 550,000 da ba sa zuwa makaranta bayan gudanar da wani aikin tantance gidaje a faɗin jihar.
Ya ce daga cikin yaran da aka gano, an riga an mayar da fiye da 300,000 zuwa makarantu.
Gwamnan ya ce shirin har yanzu yana ci gaba, yana mai cewa tsarin tattara bayanai daga gidaje ya taimaka wa jihar wajen gano yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma kai musu tallafin ilimi.

Source: Original
Ya ƙara da cewa amfani da sahihan bayanai na bai wa gwamnati damar mayar da hankali kan wuraren da matsalar yara marasa zuwa makaranta ta fi kamari, maimakon gudanar da shirye-shirye ba tare da sanin ainihin adadin waɗanda abin ya shafa ba.
Uba Sani ya zabi mataimaki
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da Jerry Adams, a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaben shekarar 2027.
Gwamna Uba Sani ya ce ya dauki matakin ne bayan gudanar da tuntuba da dama, nazari mai zurfi da kuma addu'o'i.
Asali: Legit.ng

