Yan Kano Sun Yi wa Birtaniya Martani bayan Sanarwar da Ta Fitar game da Jihar
- Gwamnatin Kano ta ce jihar na cikin aminci, tana mai watsi da gargadin tafiye-tafiye da Birtaniya ta yi wa 'yan kasarta da ke Najeriya
- Mazauna Kano sun yi watsi da gargadin, suna cewa ba shi da tushe kuma wata hanya ce ta haifar da tsoro tsakanin jama'a
- Kwamishinan Yaɗa Labarai Ibrahim Waiya ya bukaci Birtaniya da Amurka su tuntubi hukumomin tsaro kafin fitar da irin waɗannan shawarwari ga 'yan ƙasarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnatin Kano ta yi watsi da gargadin tafiye-tafiye da Birtaniya ta fitar kwanan nan ga 'yan ƙasarta da ke zaune a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa Kano na cikin aminci da tsaro, yayin da wasu mazauna jihar suka ce gargadin ba shi da tushe.

Source: Facebook
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Ibrahim Waiya, ya ce jihar ba ta cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro, cewar Punch.
Mazaunan sun bayyana gargadin a matsayin wata sanarwa marar tushe da za ta iya haifar da tsoro tsakanin 'yan Najeriya da sauran 'yan ƙasashen waje.
Kwamishinan ya ce wannan lambar yabo ta nuna ci gaban da gwamnatin Abba Yusuf ta samu wajen samar da tsaro na cikin gida, tallafa wa hukumomin tsaro da kuma shigar da matasa cikin shirye-shiryen samar da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci Birtaniya da Amurka su rika tuntubar hukumomin tsaro daban-daban da ke jihar domin samun sahihan bayanai game da halin tsaro kafin su fitar da irin waɗannan shawarwari.
Wasu mazauna Kano da suka yi magana inda suka ce ba wannan ne karon farko da Birtaniya, Amurka da wasu ƙasashen waje ke fitar da irin wannan gargadi ba.
A cewarsu, gargadin na iya kasancewa yana da alaƙa da babban zaɓen da ke tafe a Najeriya.
Ɗaya daga cikin mazaunan, Abubakar Abdullahi, ya tuna cewa a lokacin da hare-haren Boko Haram suka yi kamari a zamanin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Amurka ta sha fitar da irin waɗannan gargadi ga 'yan ƙasarta.
Abdullahi ya ce duk da gargadin da aka yi a wancan lokacin, babu wani abu makamancin abin da gargadin ya nuna da ya faru.
Wani mazaunin, Lawan Yahaya, shi ma ya bayyana gargadin a matsayin wani yunƙuri na haifar da fargaba tsakanin mazauna jihar, musamman 'yan ƙasashen waje.
Ya ce:
“Ba wannan ne karon farko da Birtaniya ko Amurka ke fitar da irin wannan gargadi ba. Sun taba fitar da irin waɗannan shawarwarin tafiye-tafiye ga ’yan ƙasarsu kafin babban zaɓen 2015, 2019 da ma 2023, amma daga baya babu wani abin da ya faru.
“Yanzu kuma da babban zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa, sun sake farawa. Wannan gargadi ne kawai marar tushe, kuma babu abin da zai faru da yardar Allah."
Ya ce Birtaniya da Amurka sun taba fitar da irin waɗannan gargadi kafin zaɓukan 2015, 2019 da 2023, amma babu abin da ya biyo baya.
Yahaya ya ƙara da cewa yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa, an sake fitar da irin wannan gargadi, wanda ya kira gargadi marar amfani.
Abba Kabir ya ba da hutun Takutaha
An ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Satumban 2026, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan Takutaha.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da hutun domin bai wa mazauna Kano damar halartar wannan gagarumin biki a fadin jihar.
Gwamnatin Kano ta bukaci ma'aikata da al'umma su yi amfani da ranar wajen addu'o'in neman zaman lafiya da ci gaban Kano da Najeriya.
Asali: Legit.ng


