Tsohon Kwamishinan INEC Ya Saka Atiku da Tinubu a Sikeli, Ya Fadi Wanda Zai Lashe Zaben 2027

Tsohon Kwamishinan INEC Ya Saka Atiku da Tinubu a Sikeli, Ya Fadi Wanda Zai Lashe Zaben 2027

  • Tsohon kwamishinan INEC, Lai Olurode, ya ce Bola Tinubu na da kyakkyawar damar sake lashe zaben shugaban ƙasa na 2027 da gagarumar nasara
  • Ya danganta hasashen nasa da inganta tsaro, ayyukan more rayuwa da kuma yadda gwamnatin Tinubu ke ɗaukar matakai masu wahala
  • Olurode ya ce sakamakon zaɓen Osun ba ya nufin ƙin amincewa da Tinubu, yana mai cewa masu zaɓe na iya raba ra’ayinsu kan shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon farfesa a fannin ilimin zamantakewa kuma tsohon kwamishinan Hukumar Zaɓe Mai Zaman kanta (INEC), Lai Olurode, ya yi hasashe kan zaben 2027.

Farfesa Olurode ya yi hasashen cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Shugaban kasa Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Olurode ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken "Hasashe na kan yunkurin tazarcen Shugaba Bola Tinubu," wadda aka wallafa ta hanyar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan kwamitin kamfen din Tinubu, ya aika sako ga Sanata Yari

Tinubu ya samu damar lashe zaben 2027

Ya ce damar Tinubu ta sake samun wa’adi na biyu ta ƙaru saboda samun kyakkyawan yanayin siyasa, ingantacceb tsaro da kuma yadda gwamnatin ke ɗaukar matakan da ba su da sauƙi.

A cewarsa, shugaban ƙasar ya nuna ƙarfin hali na siyasa a lokacin da ya ci gaba da amfani da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2023, duk da adawar da aka yi wa tsarin.

Ya kuma ce ya kamata a duba nasarar Tinubu a zaɓen 2023 bisa yanayin siyasar da ake ciki a lokacin, yana zargin cewa wasu ‘yan jam’iyyar APC sun yi aiki a kan burinsa.

“Babu ƙarfin gwamnatin tarayya da aka yi amfani da shi wajen taimaka masa. Har wasu gwamnoni jihohi sun ɗauke shi kamar kuturu a siyasa, kuma suna tsoron bayyana goyon bayansu gare shi a fili,” in ji shi.

Abin da ya faru a Osun

Olurode ya kuma yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa kayen da APC ta sha a zaɓen gwamnan jihar Osun na baya-bayan nan na nufin jama’a sun juyawa Shugaba Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tun kafin lokaci, an kammala tsara wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Olurode ya ce yana Osun a lokacin zaɓen kuma ya lura cewa wasu masu zaɓe na iya bambance tsakanin goyon bayansu ga shugaban ƙasa da kuma wanda suke so ya jagoranci gwamnatin jihar.

Tallafin man fetur da tsaro

Tsohon kwamishinan INEC ɗin ya yabawa Tinubu kan cire tallafin man fetur, yana mai cewa shugaban ƙasar jagora ne da ke shirye ya ɗauki matakai masu wahala maimakon dogaro da abin da zai faranta ran jama’a kawai.

Ya kuma yabawa gwamnatin kan inganta tsaro, yana mai cewa tattara bayanan sirri da ayyukan sojoji sun taimaka wajen raunana ayyukan ‘yan bindiga.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Dangane da ayyukan more rayuwa kuwa, Olurode ya ce gwamnatin Tinubu ta kusa kammala gina ko gyaran tituna masu tsawon kusan kilomita 6,000 cikin ƙasa da shekaru huɗu.

APM ta hango faduwar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APM ta bayyana gwamna jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin dan takarar da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Jam’iyyar ta buƙaci Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ‘yan takara su ajiye muradun kansu domin samar da ɗan takara guda a tsagin adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262