'Akwai Dalili': Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Motocin Mutane Fiye da 80 a Kano

'Akwai Dalili': Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Motocin Mutane Fiye da 80 a Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta kama motoci 81 masu lambar rajista da aka rufe, aka lalata ko kuma marasa rajista saboda matsalolin tsaro
  • Kwamishinan 'yan sanda ya ce an wayar da kan jama'a sosai kafin fara samamen, saboda haka babu wanda zai yi ikirarin cewa bai sani ba
  • 'Yan sanda sun kama wasu motoci uku wadanda ke cike da ayar tambaya, indada bincike ke gudana domin gurfanar da waɗanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama motoci 81 da aka samu suna zirga-zirga da lambar da aka rufe, aka lalata ko kuma ba su da rajista, tare da gargadin cewa za a gurfanar da masu su a kotu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce wannan lamari na barazana ga tsaron jama'a.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: 'Yan sanda sun cafke rikakkun 'yan fashi da makami a Gombe

'Yan sanda sun kama motoci 81 a Kano
Wani dan sanda yana tsaye a filin da aka ajiye motocin da 'yan sandan Kano suka kama. Hoto: Abudllahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Dalilin fara kama motoci a Kano

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa bidiyon jawabin kwamishinan 'yan sandan a shafinsa na Facebook.

A cikin bidiyon, CP Bakori ya ce rundunar ta lura da karuwar motocin da ke amfani da lambobin rajista da aka rufe ko aka lalata domin ɓoye asalinsu.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce batagari na amfani da irin waɗannan motoci wajen aikata miyagun laifuffuka tare da tserewa ba tare da an gano su ba.

An kama wasu motoci 3

Ya bayyana cewa kafin fara wannan samame, rundunar ta gudanar da yaƙin wayar da kai ta rediyo, talabijin, kafafen sada zumunta da shirye-shiryen tattaunawa kai tsaye domin sanar da masu ababen hawa wajibcin yin rajista da kuma nuna lambobin rajista yadda ya kamata.

Kwamishinan ya ce jami'an tsaro sun kuma kama wasu motoci uku a cikin yanayi mai cike da zargi, inda mutanen da ke cikinsu suka kasa bayar da gamsasshen bayani kan mallakar motocin da kuma dalilin amfani da su.

Kara karanta wannan

Daga taimako, ƴan bindiga sun bindige tsohon sojan Najeriya kusa da Abuja

Ya ce ana ci gaba da bincike kan motocin da mutanen da aka kama, yana mai jaddada cewa za a tabbatar doka ta yi aiki a kansu idan aka same su da laifi.

Ana binciken wasu motoci 3 da aka kama a Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori yana jawabi kan motocin da aka kama. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kira ga masu ababen hawa a Kano

CP Bakori ya jaddada cewa manufar wannan mataki ba tsangwama ba ce, illa tabbatar da tsaron jama'a da kuma sauƙaƙa gano duk wata mota da ke amfani da hanyoyin jihar.

Ya yi kira ga masu ababen hawa da su tabbatar sun yi rajistar motocinsu tare da sanya ingantattun lambobin rajista a bayyane domin kauce wa fuskantar hukunci.

An kama 'barawon' motar gidan gwamnati

A wani labari, mun ruwaito cewa, bincike ya fara bankado masu hannu a satar motar ayarin mataimakin gwamna da aka yi a gidan gwamnatin jihar Kano.

Dakarun yan sanda da jami'an wasu hukumomin tsaro sun kama mutum daya da ake zargi kuma sun kwato motar da aka sace.

Bayanai daga ofishin mataimakin gwamnan Kano sun nuna cewa wanda aka kama, direba ne da ke aiki a gidan gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com