Yadda Sojoji Suka Ceto Bayin Allah a Kebbi da Wasu Jihohi 2 daga Yan Bindiga

Yadda Sojoji Suka Ceto Bayin Allah a Kebbi da Wasu Jihohi 2 daga Yan Bindiga

  • Dakarun Operation Fansan Yamma sun ceto fararen hula biyar a jihar Sokoto bayan sun dakile harin kwanton bauna da ’yan ta’adda suka kai masu
  • Sojoji sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi, yayin da suka kubutar da wasu mutane biyu da suka jikkata a Zamfara
  • Rundunar ta ce tana ci gaba da farautar ’yan ta’addan da suka tsere, tare da kira ga jama’a da su rika bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun ceto fararen hula 10 a wasu samamen da suka gudanar a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Sojoji sun yi nasara a kan yan bindiga da dama
Wasu daga cikin sojojin Najeriya Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Punch ya ce ayyukan na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na kare rayukan jama’a da tabbatar da tsaron al’ummomi a yankin Arewa maso Yamma.

An ceto mutane a jihohin Arewa

Daily Post ta wallafa cewa a ranar 19 ga Agusta, sojojin da ke sintiri a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto sun yi arangama da ’yan ta’adda da suka yi musu kwanton bauna.

Rundunar ta ce yayin arangamar, an ceto fararen hula biyar tare da mika su ga iyalansu. Haka kuma, sojojin sun kwato babura biyu da ’yan ta’addan suka bari a yayin tserewarsu.

A ranar 18 ga Agusta, 2026 sojoji sun gudanar da wani samame na ceto mutane a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi, bayan samun bayanan sirri cewa an yi garkuwa da wasu mutane uku.

An yi nasara a samamen inda sojojin suka ceto dukkan mutanen uku, sannan suka tantance su tare da mika su ga hukumomin yankin da suka dace.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

Ac kubutar da mutane a Zamfara

Haka kuma, a ranar 18 ga Agusta, 2026 sojoji sun mayar da martani kan rahotannin ayyukan ’yan ta’adda a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.s

An samu nasarar lallasa yan ta'adda a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar ta ce gaggawar tura sojojin zuwa yankin ta tilasta wa ’yan ta’addan tserewa, inda suka bar wasu mutane biyu da suka yi garkuwa da su.

Mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga yayin da suke hannun ’yan ta’addan, kuma nan take aka kwashe su zuwa wani asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Sojoji sun yi wa yan bindiga rubdugu

A baya, mun kawo labarin cewa an samu nasarar hallaka ‘yan bindiga sama da 20 bayan jami’an tsaro sun dakile yunkurin sace mazauna kauyen Gidan Bawa da ke Kandarawa a jihar Katsina.

Kimanin ‘yan bindiga 40 da ke biyayya ga Isiya Kwashen Garwa ne suka mamaye kauyen da nufin sace mata da yara tare da kokarin haurawa da su cikin daji da da nufin garkuwa da su

Jami’an tsaro sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kwato shanu 19 da aka sace bayan kazamin artabun da suka yi da 'yan bindigan har aka yi galaba a kansus

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng