Maulidin Annabi SAW: Matawalle Ya ba Musulmi Shawara ana Shirin Zaben 2027
- Kungiyar Matawalle Political Movement ta taya Musulman Zamfara da Najeriya murnar Maulidin Annabi Muhammad SAW da ake yi
- Ta ce koyarwar Annabi Muhammad kan zaman lafiya, haɗin kai da ƙauna ya kamata ta zama jagora ga Musulmi a rayuwarsu
- MPM ta kuma yi kira ga Musulmi su yi addu’ar samun zaman lafiya a Zamfara da Najeriya, musamman yayin da ƙasar ke shirin yin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata kungiya da ake kira Matawalle Political Movement (MPM) ta yi martani kan bikin Maulidin Annabi SAW.
Kungiyar ta taya Musulman Zamfara da Najeriya murnar bikin Maulidin Annabi Muhammad na shekarar 1448, tare da kira da su yi koyi da koyarwarsa.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Ministan Ƙasa na Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, MPM ta ce bikin Mauludi lokaci ne na tunawa da koyarwar Annabi, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fitar da saƙo ga masu murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW a Najeriya
Matawalle ya bayyana halayen Annabi SAW
Ƙungiyar ta ce bikin ya bai wa Musulmi damar yin tunani kan koyarwar Annabi Muhammad game da zaman lafiya, haɗin kai da ƙaunar juna.
MPM ta bayyana cewa koyarwar Annabi Muhammad da tausayi da ya nuna sun shafi dukkan fannoni na rayuwar ɗan Adam, don haka ya kamata su zama jagora ga Musulmi.
Ta yi kira ga Musulmi su yi amfani da wa’azuzzuka da zaman addu’o’in Mauludi wajen roƙon Allah Ya dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da Najeriya, cewar Vanguard.
MPM ta ce bikin na bana ya zo ne a wani muhimmin lokaci, yayin da Najeriya ke shirin shiga wani sabon zagayen zaɓe, lamarin da ya sa addu’ar zaman lafiya da tsaro take da muhimmanci.
Ta ce:
“Mu yi amfani da wa’azuzzukan Mauludi da zaman addu’o’i wajen roƙon Allah Ya dawo da zaman lafiya a ƙasarmu ta ƙaunatacciya da Najeriya baki ɗaya.
“Za ku fahimci cewa a wannan lokaci mai muhimmanci, mu da babbar ƙasarmu muna matuƙar buƙatar addu’a, domin Allah Ya ci gaba da shiryar da mu a lokacin zaɓe, inda babu wanda zai fuskanci wata barazana.”

Source: UGC
Shawarar Matawalle ga al'ummar Musulmi
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Musulmi su roƙi Allah Ya ba da shiriya a lokacin zaɓe, tare da yin aiki domin samar da yanayi da babu ɗan ƙasa da zai fuskanci barazana ko tsoratarwa.
Haka kuma, ta bukaci Musulmi su riƙe kyawawan halayen Annabi Muhammad, tare da neman taimakon Allah wajen magance matsalolin da ke addabar Zamfara da Najeriya.
A ƙarshe, MPM ta yi addu’ar Allah Ya sanya bikin Mauludi ya zama alheri ga Musulmi, Ya kuma kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da Najeriya.
Tinubu ta taya Musulmi bikin Maulidi
Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin musulmi zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
Tinubu ya bukaci Musulmi su yi koyi da sadaukarwa, hakuri, juriya da tawali’u na fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW
Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya su yi addu’ar kawo karshen rashin tsaro tare da taimakon marasa karfi a wannan lokaci.
Asali: Legit.ng
