Tinubu Ya Yi Magana kan Ranar Hausa Ta 2026, Ya Fadi Matsayin Hausawa
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana Hausawa a matsayin manyan ginshikai da ke taka muhimmiyar rawa wajen hadin kai da ci gaban Najeriya
- Tinubu ya ce harshen Hausa ya bunkasa sosai, inda ya zama daya daga cikin manyan harsunan hadin kai da kasuwanci a duniya
- Shugaban kasar ya taya al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana al'ummar Hausawa a matsayin manyan ginshikai da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hadin kai da ci gaban kasar.
Ya kuma yabawa harshen Hausa, yana mai cewa harshen ya bunkasa matuka har ya zama babban harshen hadin kai da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya, wanda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agusta, 2026.
Tinubu ya yabawa harshen Hausa
Tinubu ya taya dimbin al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, yayin da ake gudanar da bukukuwa a wurare daban-daban na duniya.
Ya ce:
"Al'ummar Hausawa manyan ginshikai ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen hadin kai da ci gaban Najeriya.
"Ba tare da wata shakka ba, harshen Hausa ya bunkasa kuma ya zama daya daga cikin manyan harsunan hadin kai da kasuwanci a fadin duniya."
Tinubu ya kuma bayyana farin cikinsa kan yadda ake gudanar da bikin Ranar Hausa a fadar Sarkin Daura, yana mai taya Hausawa murnar wannan rana.
Abin sani kan Ranar Hausa
Ranar Hausa ta Duniya rana ce da aka ware duk shekara a ranar 26 ga watan Agusta domin nuna muhimmancin yaren da bunkasar da ya yi.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano
An fara bikin ne a matsayin wani yunkuri da aka kaddamar a kafafen sada zumunta domin karfafa amfani da harshen Hausa a intanet da kuma fadakar da jama'a kan muhimmancin al'adu da harshen Hausawa.
Daily Tust ta wallafa cewa dan jarida Abdulbaki Aliyu Jari ne ya fara wannan yunkuri, wanda daga bisani ya bunkasa zuwa wani babban biki da ake gudanarwa a kasashe daban-daban.

Source: Facebook
A yanzu, ana gudanar da bukukuwan Ranar Hausa a kasashen Afirka, Turai, Gabas ta Tsakiya, Asiya da kuma nahiyar Amurka.
Ndume ya yabawa Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Mohammed Ali Ndume ya ce Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan jami'ai sun taka muhimmiyar rawa wajen dawowarsa takarar Sanatan Borno ta Kudu a zaben 2027.
Ndume ya bayyana cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, sun nuna goyon baya wajen tabbatar da shigar sunansa cikin jerin masu neman tikitin APC.
Sanatan ya ce tun farko ba a sanya sunansa cikin jerin sunayen da aka gabatar domin neman tikitin takarar Sanatan Borno ta Kudu ba, amma ya ce Tinubu ya tsaya tsayin daka wajen ganin an saka sunansa.
Asali: Legit.ng
