Ba yadda Ake Tsammani ba, Gwamna Ya Fadi Silar Rashin Tsaro a Yankinsa

Ba yadda Ake Tsammani ba, Gwamna Ya Fadi Silar Rashin Tsaro a Yankinsa

  • Gwamna Hyacinth Alia ya gano babban abin da ke kara dagula tsaron jihar Benue yayin da ake fama da hare-hare
  • Ya bukaci sarakuna da mazauna yankin su kare filayen kakanninsu, tare da hana ayyukan da za su jefa al’umma cikin da tashin hankali
  • Alia ya yabawa Tinubu kan amincewa da rundunar Sojojin Najeriya ta biyar, tare da bayyana cewa hakan zai ƙarfafa tsaro a Benue

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kwande, Benue - Gwamnan Benue, Rabaran Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da sayar da filayen kakanni domin haƙar zinariya da sauran ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Alia ya yi gargadin cewa haƙar ma’adinai ba tare da tsari ba na lalata muhalli, tare da samar da yanayin da ka iya ƙara aikata laifuka da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata da 'yan bindiga suka sace masallata a Neja, ya bayar da umarni

Gwamna ya fadi silar rashin tsaro a Benue
Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue. Hoto: Fr. Alia Iormen Hyacinth.
Source: Twitter

Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sir Tersoo Kula, ya ce Alia ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a wani taron tattaunawa da jama’a a Adikpo, Kwande wanda ya wallafa a Facebook.

Abin da ke haddasa rashin tsaro a Benue

A cewar Alia, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ta taimaka wajen ƙara matsalolin tsaro a wasu sassan Kwande, yana mai cewa masu yin hakan suna aiki saɓanin muradun jihar.

Ya buƙaci shugabannin al’umma da mazauna yankin su kare filayen kakanninsu, tare da ƙin ayyukan da ka iya yin illa ga tsaron al’ummarsu.

Alia ya yi kira da a ƙara sa hannun al’umma wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da jan hankalin sarakunan gargajiya da mazauna yankin.

Gwamnan ya buƙaci sarakunan gargajiya su taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar matasa da yaƙi da munanan ɗabi’u da ka iya lalata zaman lafiya.

Ya ce irin waɗannan ɗabi’un na iya raunana haɗin kan al’umma da kuma barazana ga kyawawan al’adu da dabi’un gargajiyar yankunan.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin DSS, sojoji sun rika aman wuta a kan yan bindiga a Sokoto

Alia ya bayyana sarakuna a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen samar da tsaro a jihar, saboda rawar da suke takawa wajen gano barazana.

Ya ce sarakunan suna cikin matsayi na musamman wajen gano barazanar da ke tasowa, samar da bayanan sirri masu amfani da kuma hana aikata laifuka.

An yaba wa Bola Tinubu kan kokarinsa game da tabbatar da tsaro
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Aiswaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Yabon da Tinubu ya sha kan tsaro

Dangane da kayayyakin more rayuwa na tsaro, Gwamna Alia ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da kafa Rundunar Sojojin Najeriya ta Biyar.

Ya ce wannan mataki zai ƙarfafa ayyukan sojoji tare da inganta ɗaukar matakan tsaro a sassa daban-daban na Benue.

Gwamnan ya bayyana cewa za a kafa rundunonin Sojoji a Adikpo da Anwase domin ƙara kasancewar jami’an tsaro da kuma inganta martani ga sabbin barazana.

Ya jaddada cewa tura sojoji kaɗai ba zai isa ba, domin dole ne mazauna yankin, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai.

Gwamnan ya danganta yaƙi da rashin tsaro da bunƙasar tattalin arziki, yana mai tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da rage musu wahala.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

Miyagu sun hallaka direban Dangote a Benue

Kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga a jihar enue wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a wani mummunan hari.

Dakarun Operation WHIRL STROKE sun gano gawarwakin mutanen biyu a cikin motar Dangote yayin sintirin dare a yankin Igbayima.

Sojoji sun kwato harsasai 11 da aka harba tare da fara farautar waɗanda ake zargi domin dakile hare-hare a hanyar Kyado–Jootar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.