Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta

Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, an kaure da fada tsakanin Hausawa da Fulani a jihar Delta
  • Lamarin ya faru ne sakamakon wani rashin fahimta da aka samu tsakanin wani yaron Hausawa da na Fulani
  • An ce Bafulatani ya caka wa wani yaron Hausawa wuka ne, lamarin da ya jawo fadan daukar fansa daga Hausawa

Delta - Rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan da Fulani makiyaya a jihar Delta
Taswirar jihar Delta | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.

Meye ya hada Hausawa da Fulani fada?

An tattaro cewa kabilun sun fara gwabza fada ne a daren ranar Lahadi 29 ga watan Agusta bayan da wani Bafulatani makiyayi ya caka wa wani yaro Bahaushe dan jihar Nasarawa wuka a daji, inda ya garzaya gida da raunuka.

A fusace da wukake, Hausawa a kasuwa, musamman 'yan jihar Nasarawa, an ce sun gaggauta shirin daukar fansa da kai farmaki kan Fulani makiyaya a cikin daji.

Amma an ba da rahoton cewa Fulanin sun taresu da muggan makamai, lamarin da ya haifar da rikici wanda ya kai har ma mutanen da ba 'yan Arewa ba suka tsere domin neman tsira.

Kara karanta wannan

Har yaran masu kudi muna kamawa, Shugaban hukumar Hisbah

A halin da ake ciki, jami'an 'yan sanda daga ofishin 'yan sanda na Sapele karkashin jagorancin CSP Harrison Nwaboisi sun shiga cikin lamarin ta hanyar tura jami'an tsaro zuwa wurare masu mahimmanci da nufin kawar da tashin hankali da hana rura wutar rikicin.

Da yake tsokaci kan lamarin, wani dan kasuwa a kasuwar, Ibrahim Umoru, ya shaidawa manema labarai cewa rikicin ya samo asali ne bayan da wani Bafulatani ya caka wa wani Bafulatani wuka saboda ya same shi a kewayen sansanin su.

A cewar Bahaushen:

“Watakila shi (Bafulatanin) ya yi tunanin yaron ya zo ya yi musu sata ne. Bai tambayi dalilin da ya sa (yaron) yake wurin ba.
"Al'amarin ya zo mana da safiyar yau kuma ba za mu iya zama kawai mu zuba ido muna ganin yadda suke kai mana hari a kowane lokaci ba. Muna so mu fada masu cewa mu ba wawaye bane."

Wani Bafulatani makiyayi da ya yi magana da manema labarai inda ya nemi a sakaya sunansa, ya zargi Hausawa da haddasa rikicin amma bai yi karin bayani ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya

Ba a iya jin ta bakin mukaddashin Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda, DSP Edafe Bright ba dangane da lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin, Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Asali: Legit.ng

Online view pixel