'Yan Bindiga Sun kai Hari Fadar Sarki ana Tsaka da Bikin Gargajiya, an Tarwatse
- Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta fara bincike bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari fadar basaraken garin Finima da ke karamar hukumar Bonny
- Basaraken Finima, Dagogo Brown, ya tsallake rijiya da baya bayan maharan sun shiga wurin wani bikin gargajiya suna harbe-harbe
- 'Yan sanda sun tabbatar da kama mutum daya daga cikin wadanda ake zargi, yayin da ake ci gaba da neman sauran maharan da suka tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers – Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta fara bincike kan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai fadar basaraken garin Finima da ke karamar hukumar Bonny.
An rahoto cewa Amadabo na Finima, HRH Dagogo Brown, ya tsallake rijiya da baya bayan maharan sun afka wani wurin gudanar da al'adun gargajiya tare da yin harbe-harbe.

Source: Original
Punch ta wallafa cewa Harin ya faru ne a ranar Asabar, inda aka ce maharan sun kuma lalata wasu kadarori tare da jikkata wasu mazauna yankin.
An kai hari fadar sarki a Rivers
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani kan wasu al'adun gargajiya, wasan gargajiya na masu na wasu mutane da abin da ya shafi hakkin wasu iyalai na gudanar da wasu bukukuwa.
Ana zargin cewa sabanin ya rikide zuwa tashin hankali a farkon ranar Asabar, inda 'yan bindiga suka shiga yankin tare da bude wuta.
Duk da cewa ba a samu rahoton mutuwar kowa ba, wasu mazauna yankin sun samu raunukan harbin bindiga da kuma sara da adda.
Bayan aukuwar lamarin, an tura jami'an tsaro zuwa yankin domin kwantar da tarzoma da tabbatar da zaman lafiya.
An kama mutum daya
PM News ta wallafa cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Rivers, ASP Blessing Agabe, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa ta ce rundunar ta fara bincike domin gano tare da cafke duk wadanda ke da hannu a harin.
Agabe ta bayyana cewa an riga an kama mutum daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a harin da aka kai fadar sarkin.

Source: Twitter
Ta ce wanda aka kama yana bai wa jami'an tsaro bayanan da za su taimaka wajen ci gaba da bincike da gano sauran wadanda ake nema.
A cewar kakakin rundunar, dakarun 'yan sanda na ci gaba da kokarin cafke sauran wadanda ake zargin da suka tsere.
'Yan bindiga sun sace matar sarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai sabbin hare-hare a wasu yankuna na jihar Kwara tare da yin garkuwa da mutane da dama.
Daga cikin wadanda aka sace akwai matar sarkin garin Dabu da ke karamar hukumar Ifelodun, wadda aka fi sani da Iya Ayoka.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma sace wasu mazauna yankuna daban-daban, ciki har da mata da wani yaro, lamarin da ya kara tayar da hankulan jama'a kan matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng

