N700,000 don Samun Mace? Babban Malami Ya Ƙaddamar da Shafin Hada Aure a Najeriya
- Fitaccen limamim coci a Najeriya, Fasto Kingsley Okonkwo ya kaddamar da shafin Mentor To Marry domin hada marasa aure da ke neman aure
- Ya ce dangantakar soyayya a zamanin yanzu ta koma neman riba maimakon gina kyakkyawar abota
- Masu neman aure za su iya zabar tsarin rajista na Regular, Premium ko VIP da kudinsu ya kai N70,000, N350,000 da N700,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos – Fasto Kingsley Okonkwo, mai ba da shawara kan harkokin soyayya kuma babban limamin cocin DCC, ya kaddamar da wani shafi da zai taimaka wajen hada marasa aure da ke neman sbokan zama.
Faston ya ce alakar soyayya a wannan zamani ta koma wani abu da ake kasuwanci da shi, lamarin da ya sanya wasu samari ke fuskantar matsala wajen samun matan da za su aura.

Source: Instagram
Okonkwo ya bayyana kaddamar da shafin ne ta wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na X, lamarin da ya tada kura tsakanin matasa a kafafen sada zumunta.
Dalilin kafa shafin hada aure
Ya bayyana cewa dangantakar da ake samu a tsakanin matasa maza da mata a wannan zamani ta fi karkata ga neman kudi maimakon gina kyakkyawar alaka da fahimtar juna.
A cewar Okonkwo, shafin ya kasa maza masu matsayi daban-daban damar neman abokiyar aure.
Ya sanya wa shafin suna Mentor To Marry. A cewarsa, shafin wata al’umma ce da ke hada kiristocinmasu neman aure da gaske.
Nawa ake biya?
Binciken da Legit Hauss ta gudanar a shafin ya nuna cewa masu neman shiga domin neman matar aure za su iya zabar daya daga cikin tsare-tsare uku na rajista.
Tsarin Regular: Ana biyan N70,000 domin rajista, sannan mutane za su halarci azuzuwan horaswa na tsawon makonni takwas. Za su kuma samu damar duba wasu bayanan masu neman aure, amma damar za ta kasance mai iyaka.
Tsarin Premium: Ana biyan N350,000 domin rajista. Masu wannan tsarin za su samu karin damar da wadanda ke cikin tsarin Regular ba su da su, ciki har da kasancewa cikin wata kungiya ta musamman.
Tsarin VIP: Masu wannan tsarin za su biya N700,000 domin rajista, inda za su samu damar duba bayanan masu neman aure daga sassa daban-daban na duniya.

Source: Twitter
Mutane sun yiwa Fasto raddi
Sai dai wannan abu da Faston ya yi jawo masa suka daga mutne da dama, inda wasu ke ganin ya cika kudin cajina shafin hada auren.
@OurFavOnlineDoc ya yi martani da cewa:
"Wani “mutumin Allah” a Najeriya na karɓar kuɗi daga maza domin haɗa su da mata ta shafinsa na intanet.
"Fasto yana neman mutum ya biya N700,000 domin haɗa shi da mata da kuma samun “damar ganawa da faston”. To, mene ne bambancin wannan da abin da masu safarar mata ke yi?"
@AyoAppeal ya ce:
"Me ya sa farashin ya yi tsada haka, Dala $260 da $520, don kawai samun damar amfani da shafin Pastor na musamman? Wane amfani ne hakan zai ƙara wa marasa aure da ke neman abokin rayuwa?"
An kama Fasto da laifin lalata da mata
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta samu babban limamim coci, Fasto Ajiboye Olayinka da laifin dirka wa kananan yara mata da aka ba shi amana ciki a wurin ibada a Kwara.
Sakamakon haka, mai shari'a Hammed Gegele na babbar kotun jihar Kwara ya yanke masa hukuncin kare ragowar rayuwarsa a gidan gyaran hali
Asali: Legit.ng


