Gwamnoni Sun Fito da Magana da ake Zargin Sun Handame Kudin Tallafin Mai

Gwamnoni Sun Fito da Magana da ake Zargin Sun Handame Kudin Tallafin Mai

  • Gwamnoni sun yi watsi da zargin cewa gwamnatocin jihohi sun kasa yin bayani kan yadda suka kashe kuɗin da aka samu bayan cire tallafin mai
  • Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce tana duba wani sabon shiri na amfani da motocin CNG domin rage kuɗin sufuri da sauƙaƙa wa talakawa
  • Rahoto ya ce gwamnonin sun ce rage kuɗin sufuri zai taimaka wajen rage tsadar abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnonin jihohi 36 karkashin kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, sun yi watsi da zargin cewa gwamnatocin jihohi sun kasa yin cikakken bayani kan yadda suka gudanar da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana hakan ta bakin gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, bayan taron da kungiyar ta gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

An taso gwamnoni a gaba bayan FAAC ta cika aljihunsu da N47tr

Gwamnonin Najeriya a Abuja
Lokacin da gwamnonin jihohi suka yi taro a Abuja. Hoto: NGF
Source: Twitter

Tribune ta rahoto cewa Gwamna Diri ya ce ba gaskiya ba ne a daura wa gwamnatocin jihohi alhakin rashin yin bayani kan yadda aka gudanar da kuɗin cire tallafin mai.

Martanin gwamnonin Najeriya

Da aka tambaye shi ko gwamnatocin jihohi za su amince da zargin cewa ba su yi cikakken bayani kan yadda suka kashe kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur ba, Gwamna Diri ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce:

"Hakan ba zai iya zama gaskiya ba. Hakan ba zai iya zama gaskiya ba, amma za mu bar wannan muhawarar zuwa wata rana."

Gwamnonin sun kuma bayyana goyon bayansu ga wani sabon shirin da suka kira NACTP, wanda ake shirin aiwatarwa karkashin jagorancin gwamnatocin jihohi.

Shirin CNG zai rage kuɗin sufuri

Gwamna AbdulRazaq ya ce shirin zai taimaka wajen amfani da ƙarancin kuɗin tafiyar da motocin CNG domin rage kuɗin zirga-zirgar fasinjoji a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim

A karkashin shirin, ana tunanin gwamnatocin jihohi za su bayar da tallafi wajen sauya motocin zuwa tsarin CNG, samar da motocin haya da kuma gina abubuwan more rayuwa da ake bukata.

Leadership ta wallafa cewa ya ce kuma za a bukaci masu gudanar da harkar sufuri da za su shiga shirin su yi alkawarin rage kuɗin fasinjoji domin amfanin jama'a.

Gwamnonin sun ce rage kuɗin sufuri zai haifar da tasiri mai kyau ga sauran bangarorin tattalin arziki, musamman saboda tsadar jigilar kaya na daga cikin dalilan tashin farashin abinci da sauran kayan masarufi.

Yadda ake sayar da mai
Ana zubawa babur fetur ana gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da yake magana kan kiraye-kirayen da ake yi na soke matakin cire tallafin man fetur, shugaban kungiyar gwamnonin ya ce shirin NACTP na daga cikin matakan da ake duba domin rage radadin cire tallafin ga talakawan Najeriya.

Gwamnoni sun kashe N512bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatocin jihohi 33 sun kashe akalla Naira biliyan 512.10 wajen gudanar da fadojin gwamnati, ofisoshin gwamnoni, tafiye-tafiye da sufuri a watanni shida na farkon shekarar 2026.

Binciken rahotannin aiwatar da kasafin kudin jihohi ya nuna cewa an ware Naira biliyan 420.01 domin fadojin gwamnati, ofisoshin gwamnoni da sauran harkokin gudanarwar bangaren zartarwa.

Haka kuma, bayanan sun nuna cewa an kashe Naira biliyan 92.09 a bangaren tafiye-tafiye da sufuri, wanda ya kai jimillar Naira biliyan 512.10 a cikin watanni shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng