Yadda Gwamnoni ke Wadaka da Kudi, Sun Kashe Naira biliyan 512 a Wasu Harkoki

Yadda Gwamnoni ke Wadaka da Kudi, Sun Kashe Naira biliyan 512 a Wasu Harkoki

  • Gwamnatocin jihohi 33 sun kashe aƙalla Naira biliyan 512.10 kan Gidajen Gwamnati, ofisoshin gwamnoni da tafiye-tafiye a farkon watanni shida na 2026
  • Adadin ya ninka jimillar albashin gwamnoni 36 na watanni shida sau fiye da 4,700, yayin da bayanai suka nuna albashinsu bai wuce N108.65m ba
  • Jihohin Kogi, Ogun da Legas ne suka fi kashe kuɗi wajen gudanar da Gidajen Gwamnati da ofisoshin gwamnoni, yayin da Plateau ta fi kashe kuɗi kan tafiye-tafiye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatocin jihohi 33 a Najeriya sun kashe aƙalla Naira biliyan 512.10 wajen gudanar da Gidajen Gwamnati, ofisoshin gwamnoni da kuma tafiye-tafiye cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.

Binciken bayanan yadda aka aiwatar da kasafin kuɗin jihohi ya nuna cewa an ware Naira biliyan 420.01 kan Gidajen Gwamnati, ofisoshin gwamnoni da sauran harkokin gudanarwar bangaren zartarwa.

Kara karanta wannan

Yadda hukumar bogi ta yi ta yaudarar gwamnoni tana neman kudi da filaye

Gwamnonin Najeriya 36 a wajen taro
Yadda gwamnonin Najeriya suka yi taro a Abuja. Hoto: NGF
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa an kashe Naira biliyan 92.09 kan tafiye-tafiye da sufuri, wanda ya sa jimillar kuɗin da aka kashe kan bangarorin biyu ta kai Naira biliyan 512.10.

Batun albashin gwamnoni

Bayanan sun nuna babban bambanci tsakanin ainihin albashin gwamnoni da kuma kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da ofisoshinsu.

Pulse Nigeia ta wallafa cewa Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce albashinsa na wata-wata N503,000 ne, inda ya ce wasu manyan ma'aikatan gwamnati suna samun N900,000 a wata.

Idan aka yi la'akari da wannan albashi, gwamna ɗaya zai samu kusan Naira miliyan 3.018 ne cikin watanni shida.

Hakan na nufin jimillar albashin gwamnoni 36 cikin watanni shida zai kai kusan Naira miliyan 108.65 kacal.

Sai dai wannan adadi ya kasance kusan sau 4,713 kasa da Naira biliyan 512.10 da aka gano cewa jihohi sun kashe kan gudanar da ofisoshin gwamnoni da tafiye-tafiye.

Binciken ya nuna cewa jimillar albashin gwamnoni 36 bai wuce 0.02% na kuɗaɗen da aka kashe kan wadannan bangarori ba.

Kara karanta wannan

Betta Edo da wasu gingima gingima da ake zargi da aka gano cikin kamfen Tinubu

Jihohin da suka fi kashe kuɗi

Binciken jiha bayan jiha ya nuna cewa jihar Kogi ce ta fi kashe kuɗi wajen gudanar da Gidan Gwamnati da ofishin gwamna, inda ta kashe Naira biliyan 65.34.

Jihar Ogun ce ta biyo baya da Naira biliyan 45.26, yayin da Legas ta kashe Naira biliyan 45.04.

Kano ta kashe Naira biliyan 25.87, Ekiti Naira biliyan 25.22, yayin da jihar Cross River ta kashe Naira biliyan 23.92.

Wajen taron gwamnoni a Najeriya
Wasu gwamnonin Najeriya a wajen taro. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

Bayelsa ta kashe Naira biliyan 22.99, Imo Naira biliyan 19.43, yayin da jihar Enugu ta kashe Naira biliyan 16.20.

A bangaren jihohin da suka kashe mafi ƙarancin kuɗi cikin bayanan da aka samu, jihar Oyo ta kashe kusan Naira biliyan 1.95, Sokoto Naira biliyan 2.20, Kwara Naira biliyan 2.59 da Abia Naira biliyan 2.78.

Batun kashe kuɗi a tafiye-tafiye

A bangaren tafiye-tafiye da sufuri, jihar Plateau ce ta fi kashe kuɗi a watanni shida na farkon 2026, inda ta kashe Naira biliyan 10.11.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Nyesom Wike bai zama darakta janar na kamfen Tinubu ba'

Legas ta biyo baya da Naira biliyan 8.23, yayin da jihar Taraba ta kashe Naira biliyan 5.16.

Jihar Niger ta kashe Naira biliyan 4.45, Ekiti Naira biliyan 4.41, Bauchi Naira biliyan 3.75, yayin da Yobe ta kashe Naira biliyan 3.68.

Oyo ta kasance cikin jihohin da suka fi kashe kuɗi kaɗan, inda aka gano ta kashe Naira miliyan 667.52, yayin da Kano ta kashe Naira miliyan 626.95.

An kara kudin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar Dangote ta kara farashin man fetur duk da shirin ta na kai man fetur kyauta zuwa wasu sassan kasar.

Binciken kasuwa ya nuna cewa gidajen man NNPCL a Abuja da kewaye sun kara farashin litar man fetur daga N1,250 zuwa N1,270.

Rahotanni sun nuna cewa karin na N15 kan kowace lita ya zo ne duk da cewa farashin danyen mai na kara sauki a kasuwar duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng