Ana Wata ga Wata: Matatar Dangote Ta Yi Barazana kan Fetur din da Take Samarwa

Ana Wata ga Wata: Matatar Dangote Ta Yi Barazana kan Fetur din da Take Samarwa

  • Matatar Dangote ta ce kusan kashi 43 cikin 100 na fetur da aka samar wa kasuwar Najeriya a watan Yuli ya fito ne daga man da aka shigo da shi
  • Kamfanin ya ce yawaitar shigo da fetur na sa samun cikakken hasashen buƙatar man fetur da tsara adadin da ya kamata a ajiye cikin wahala
  • Matatar ta yi gargadin cewa za ta iya fitar da rarar fetur zuwa kasuwannin ƙasashen waje domin guje wa tsadar ajiya da kuɗin da ake kashewa wajen riƙe man da bai samu kasuwa a cikin gida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar Man Fetur ta Dangote ta yi barazanar fitar da rarar fetur da take da shi zuwa kasuwannin ƙasashen waje, yayin da yawaitar shigo da man fetur ke haifar da rashin tabbas kan buƙatar kasuwar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Matatar Dangote ta bayyana cewa man fetur da aka shigo da shi ya kai kusan kashi 43 cikin 100 na dukkan fetur da aka samar wa kasuwar Najeriya a watan Yulin 2026.

Matatar Dangote ta koka kan shigo da fetur
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa matatar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026.

Matatar ta ce wannan na faruwa ne duk da cewa tana da ƙarfin tace isasshen fetur da zai iya biyan buƙatar Najeriya, har ma ya wuce abin da ake buƙata a cikin gida.

A cewar kamfanin, ci gaba da bayar da lasisin shigo da man fetur na sanya shi cikin mawuyacin hali wajen tsara yawan man da zai samar da kuma adadin da zai ajiye domin kasuwar cikin gida.

Dangote ta ce tana ajiye isasshen fetur

Matatar ta ce tun bayan fara aiki, ta kasance tana tabbatar da cewa tana da isasshen man fetur a ajiye domin samar da ci gaba da wadata ga kasuwar Najeriya.

Ta ce hakan ya buƙaci zuba jari mai yawa wajen samar da wuraren ajiya, sufuri da kuma kuɗaɗen gudanar da harkokin kasuwanci, The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Sai dai kamfanin ya ce rashin cikakken bayani kan yawan fetur da ake shirin shigowa da shi Najeriya na ƙara wahalar da tsarin samarwa da kuma kula da kayan da aka ajiye.

“A matsayinta na mai samar da makamashi mai ɗaukar nauyi, a koyaushe muna ƙoƙarin ajiye isasshen tanadi domin biyan buƙatar cikin gida a kowane lokaci,” in ji matatar.

Ta ƙara da cewa idan ana ci gaba da shigo da dimbin man fetur ta hanyar lasisin da hukumomin da suka dace suka bayar, alhali babu cikakken haske kan yawan man da ake sa ran shigowa da shi nan gaba, riƙe rarar man na iya zama ba shi da amfani ta fuskar kasuwanci.

Za a iya fitar da rarar fetur waje

Matatar ta bayyana cewa idan kasuwar cikin gida ba ta iya ɗaukar dukkan man da aka samar ba, za ta tilasta mata fitar da rarar man zuwa kasuwannin yankin da na duniya.

Kamfanin ya jaddada cewa ƙarin fitar da fetur zuwa ƙasashen waje ba yana nufin ta kasa biyan buƙatar Najeriya ba ne.

A maimakon haka, ta ce matakin zai kasance ne sakamakon taruwar rarar fetur saboda rashin tabbas kan adadin man da ake shigo da shi cikin ƙasar.

Kara karanta wannan

An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya

Matatar ta ce fitar da rarar man zai taimaka wajen guje wa ƙarin kuɗaɗen ajiya da na samar da jari da ake kashewa wajen riƙe fetur da bai samu kasuwa a cikin gida ba.

Matatar ta jaddada ci gaba da samar da mai

Duk da barazanar fitar da rarar fetur, kamfanin ya ce hakan ba yana nufin zai janye daga kasuwar Najeriya ba.

Matatar ta jaddada cewa har yanzu tana da niyyar tabbatar da samun isasshen fetur a sassan ƙasar, tare da ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamashi a Najeriya.

Sai dai ta yi gargadin cewa idan aka samu ƙarancin fetur a nan gaba sakamakon rikicewar kasuwa da yawan shigo da man fetur, bai kamata a ɗora alhakin hakan kan Matatar Dangote ba.

A cewar kamfanin, yawaitar shigo da fetur da kuma rashin damar matatun cikin gida na yin sahihin hasashen buƙatar kasuwa na iya haifar da matsalolin samarwa da rarrabawa a nan gaba.

Matatar Dangote ta yi barazana
Motocin dakon mai a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Matatar Dangote ta fadada shirin raba fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta sanar da faɗaɗa shirin raba man fetur da sauran kayayyakin man fetur kyauta.

Matatar ta fadada shirin ne zuwa jihohin Kano, Imo da wasu jihohi biyu, inda ta ce shirin zai rage kuɗin da 'yan kasuwar mai masu zaman kansu ke kashewa wajen safarar man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng