Matatar Dangote Ta Kara Kudin Litar Man Fetur a Najeriya
- Matatar Dangote ta kara farashin man fetur daga N1,185 zuwa N1,200 kan kowace lita, wanda ya fara aiki ranar 26 ga Agusta, 2026
- Sabon karin ya zo ne kwanaki kadan bayan matatar ta kara farashin man fetur daga N1,165 zuwa N1,185 kan kowace lita.
- Karin farashi a Najeriya na zuwa ne duk da rahotannin da ke nuna cewa farashin danyen mai ya sauka a kasuwannin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa matatar Dangote ta kara farashin man fetur daga N1,185 zuwa N1,200 kan kowace lita.
Sabon farashin ya fara aiki daga ranar Talata, 26 ga Agusta, 2026, kamar yadda matatar ta sanar da kwastomominta a wata sanarwa.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa Karin farashin ya zo ne a daidai lokacin da farashin danyen mai ke sauka a kasuwannin duniya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan dalilin karin kudin man fetur.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano
Dangote ya kara kudin mai
A wata sanarwa da sashen kula da harkokin kasuwanci na matatar Dangote ya aika wa kwastomomi ranar Talata, an bayyana sabon farashin man fetur na jigilar tankoki da kuma wanda ake kaiwa ta ruwa.
Sanarwar ta bukaci kwastomomi su lura cewa an sauya farashin man fetur na matatar, wanda ya fara aiki a ranar 26 ga Agusta.
Bayanin ya nuna cewa farashin jigilar mai ta tankoki daga matatar ya tashi daga N1,185 zuwa N1,200 kan kowace lita.
Matatar ta kuma umarci kwastomominta da su mayar da dukkan takardun ATC domin a sake tsara farashin, tare da bayyana cewa za a ba su sabuwar yarjejeniyar daukar mai domin a ci gaba da daukar man.
Karin farashin a gidajen mai
Sabon karin ya nuna an kara N15 kan kowace lita, bayan da matatar ta kara farashin daga N1,165 zuwa N1,185 kwanaki kadan da suka gabata.
Rahotanni sun nuna cewa karin farashin na ranar 21 ga Agusta, 2026, ya fara aiki daga tsakar dare kafin sabon karin da aka sanar ranar Talata.
Ana ganin sabon matakin zai iya haifar da karin farashin man fetur a gidajen mai, yayin da 'yan kasuwa za su kara kudin sufuri da sauran kudaden gudanar da harkokinsu.

Source: Getty Images
Wasu rahotanni sun nuna cewa ana iya samun matsakaicin farashin man fetur kusan N1,250 kan kowace lita idan sababbin farashin suka isa gidajen mai.
Farashin danyen mai ya sauka
Blueprint ta wallafa cewa sabon karin farashin man fetur na Dangote ya zo ne duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Bayanan da aka samu ranar Talata sun nuna cewa farashin West Texas ya sauka zuwa $82.13 kan kowace ganga, yayin da Brent ya koma d$88.37.
Dangote ya fadada raba mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa Matatar Dangote ta fadada shirinta na kai kayayyakin man fetur kyauta zuwa jihohin Kano, Imo, Anambra da Nasarawa.
Matatar ta ce shirin, wanda tun farko ya shafi Legas, Ogun, Rivers, Kaduna, Abuja da Delta, zai taimaka wajen rage kudin rarraba man fetur da 'yan kasuwa ke kashewa.
Babbar daraktar sashen harkokin kasuwanci na Dangote, Fatima Aliko Dangote, ta ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa an samu sauki a Najeriya.
Asali: Legit.ng
