An kai Hare Hare Birnin Makkah, Saudiyya Ta Dauki Matakin Gaggawa

An kai Hare Hare Birnin Makkah, Saudiyya Ta Dauki Matakin Gaggawa

  • Rundunar tsaron sararin samaniyar Saudiyya ta kakkabo wani jirgi mara matuki da kungiyar Houthi ta harba zuwa yankin Makka
  • Jirgin ya kasance yana kokarin shiga sararin samaniyar da aka haramta zirga-zirgar jiragen sama a kan birnin mai tsarki na Makka kafin aka dakile shi
  • Kakakin kawancen da ke dawo da halastacciyar gwamnati a Yemen ya ce lamarin ya faru ne a kudancin Makka da yammacin Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rundunar tsaron sararin samaniyar Saudiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi mara matuki da kungiyar Houthi ta harba, kafin ya shiga sararin samaniyar da aka haramta zirga-zirgar jiragen sama a birnin Makka.

Kakakin kawancen da ke dawo da halastacciyar gwamnati a Yemen, Manjo Janar Turki Al-Malki, ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

An rincabe da fada a Hormuz, Iran ta harbo jirgin yakin Amurka

Dakin Allah da ke kasar Saudiyya
Masu ibada a masallacin Ka'aba a Makkah. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kai hari Makkah

Rahoton Roya News ya nuna cewa Al-Malki ya ce tsarin tsaron sararin samaniyar Saudiyya ya gano tare da kakkabo jirgin a kudancin Makka da misalin karfe 6:50 na yammacin Talata, 15 ga Satumba.

Ya bayyana cewa lamarin shi ne karo na biyu da aka yi wani yunkurin kai hari kan Makka, bayan wani harin da aka yi a shekarar 2017.

A ranar 27 ga Yulin 2017, mayakan Houthi sun harba wani makami mai linzami zuwa Makka, a cewar kakakin kawancen.

Harin ya shafi wuri mai tsarki

Al-Malki ya bayyana harin a matsayin yunkurin ta'addanci da ke neman razana masu ibada, mahajjata, 'yan kasa da mazauna birnin.

Ya ce harin wani yunkuri ne na tunzura miliyoyin Musulmi a fadin duniya saboda muhimmancin Makka a matsayin wurin da wahayi ya sauka kuma alkibilar Musulmi.

Masu Ibada a dakin Ka'aba
Mutane na dawafi a masallaci mai alfarma na Makkah. Hoto: Inside Haramain
Source: Facebook

Kakakin ya ce irin wannan mataki zai kasance abin kunya da kuma wani mummunan tarihi ga kungiyar Houthi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali, kwamishina mai ci ya fadi, an tabbatar da mutuwarsa

Saudiyya ta yi gargadi

Al-Malki ya ce rundunar kawancen za ta ci gaba da kare wuraren ibada masu tsarki da fararen hula a cikin kasar Saudiyya.

Al Jazeera ta wallafa cewa ya ce:

“Ba ja da baya a kan tsaron Masallatan Harami biyu.”

Kakakin ya kara da cewa Rundunar Hadin Gwiwa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar dukkan matakan da suka dace kuma masu hana kai hare-hare kan kungiyar Houthi.

Batun harin Amurka a Iran

A wani rahoton, kun ji cewa wani mai sa ido kan ayyukan Ma'aikatar Tsaron Amurka ya bayyana cewa Amurka ta yi asarar jiragen sama da dama, ciki har da akalla jirage marasa matuki kirar MQ-9 Reaper 30, yayin yakin da Iran.

Rahoton ya ce daruruwan gine-gine da wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su sun lalace ko kuma aka lalata su sakamakon hare-haren Iran tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni.

Rahoton ya kuma ce Amurka ta kashe kimanin $22bn wajen makaman da aka yi amfani da su a yakin, yayin da jimillar kudin yakin a wannan lokacin ta kai $33bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng