Trump Ya Fitar da Gargadi game da Saudi bayan Harin Houthi a Makkah

Trump Ya Fitar da Gargadi game da Saudi bayan Harin Houthi a Makkah

  • Ma'aikatar Wajen Amurka ta bukaci 'yan kasarta da su sake tunani kafin su yi tafiya zuwa kasar Saudiyya sakamakon barazanar hararen Houthi
  • Gargadin ya fito ne bayan harharen samaniya na makamai masu linzami da jirage marasa matuka sakamakon barkewar takun saka da Houthi
  • Tawagar Pakistan a Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da harharen 'yan Houthi tare da jaddada goyon bayanta ga ikon mallakar kasa na Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Ma'aikatar Wajen Amurka a ranar Talata ta gargadi 'yan kasar da su sake tunani mai zurfi kafin gudanar da tafiya zuwa kasar Saudiyya bayan hare-haren Houthi.

Gargadin tafiyar da ma'aikatar ta fitar ya buƙaci 'yan ƙasar da su kula da barazanar harba makamai da nufin lalata muradun Amurka, rikicin sanye da makamai, ta'addanci, da kuma dokokin gida game da amfani da shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Boye boye ya kare, Amurka ta bayyana gagarumar barnar da Iran ta yi mata

Donald Trump a kasar Saudiyya
Lokacin da Donald Trump ya ziyarci Saudiyya a 2026. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Amurka ta wallafa cewa tun bayan barkewar rikici tsakanin Amurka da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, aka samu ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare.

Ya rubuta cewa:

"Biyo bayan barkewar takun saka tsakanin Amurka da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, an samu ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami daga Iran. 'Yan kasar Amurka da ke da zaman su kusa da cibiyoyin makamashi da sansanonin soji na fuskantar babban hatsari."

Ƙalubalen tsaro a Yemen

Wannan gargadi ya zo ne bayan hukumomin birnin Riyadh sun fitar da saƙonnin kariya a Makkah da sauran yankuna sakamakon zargin kai hare-hare da ƴan tawayen Houthi ke yi.

Hukumar tsaron Saudiyya ta sanar da cewa ta harbo wani jirgi mara matuƙi na ƴan Houthi a kudancin Makkah kafin ya shiga sararin samaniyar garin mai tsarki, ko da yake ƴan Houthi sun ƙaryata zargin.

Kara karanta wannan

An fara rade radin kulla sabuwar hadaka domin kifar da Tinubu a 2027

Kakakin kungiyar Houthi
Yahya Saree da ke magana da yawun Houthi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ma'aikatar Wajen Amurka ta keɓance yankin iyakar Yemen a matsayin wajen da kada a yi tafiya zuwa wajen, sakamakon haɗarin da ke barazana ga rayuka sakamakon makaman da aka harbo.

Maganar da Pakistan ta yi

Balo Pulse ta wallafa cewa ƙasar Pakistan ta gabatar da wannan rikici a gaban Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya a lokacin wani taro na gaggawa kan ƙasar Yemen.

Wakilin dindindin na ƙasar Pakistan a majalisar, Ambassador Asim Iftikhar Ahmad, ya yi Allah-wadai da hare-haren ƴan Houthi kan kasar Saudiyya, yana mai gargaɗin cewa rikicin ya kai mataki mai haɗarin gaske.

Ya jaddada cewa haɓakar hare-haren a kewayen babbar hanyar ruwa ta Bab al-Mandab na iya haifar da mummunan tasiri ga kasuwancin teku na ƙasa da ƙasa da kuma harkar samar da makamashi a duniya.

Martanin Saudi ga Houthi

A wani labarin, kun ji cewa Saudiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi maras matuki da kungiyar Houthi ta harba a kudancin Makka, kafin ya shiga sararin samaniyar Makkah.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Sai dai kungiyar Houthis ta musanta cewa ta nufi Makka da harin, inda jami’in ofishin siyasarta, Hazem al-Assad, ya bayyana zargin a matsayin karya.

Lamarin ya zo ne yayin da ake samun sabon tsanani a rikicin Yemen, inda Houthi da dakarun gwamnatin Yemen masu samun goyon bayan Saudiyya ke kara gwabzawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng