FAAC: Jihohi 5 da suka samu kaso mafi tsoka na kudaden shiga a 2020

FAAC: Jihohi 5 da suka samu kaso mafi tsoka na kudaden shiga a 2020

Najeriya ta dogara sosai a kan kudaden shiga daga man fetur, duk da cewa Allah ya albarkace ta da wasu albarkatu da dama wadanda kuma za su iya samar da karin kudade don kula da yawan mutanen da ke bunkasa.

Kowane wata, Kwamitin FAAC na raba kuɗaɗen shiga daga asusun ƙasar, asusun hada hadar kudade na FOREX da da sauran tushe na gwamnatoci uku, wato, tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

KU KARANTA KUMA: Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce

FAAC: Jihohi 5 da suka samu kaso mafi tsoka na kudaden shiga a 2020
FAAC: Jihohi 5 da suka samu kaso mafi tsoka na kudaden shiga a 2020 Hoto: @IAOkowa, @MrUdomEmmanuel, @rvsg_ng, @govdouyediri, @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Da yake tsokaci ga rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), jaridar Business Day ta ruwaito cewa a shekarar 2020, FAAC ta raba jimillar naira tiriliyan 2.49 ga gwamnatin tarayya yayin da jihohi suka samu jimlar naira tiriliyan 2.30 a cikin wannan lokacin.

Ga jerin manyan jihohi biyar da suka karbi makudan kudade daga kason da gwamnatin tarayya ta ware kowane wata, a cewar rahoton.

1. Delta - biliyan N186.828

2. Akwa Ibom - biliyan N146.265

3. Ribas - biliyan N141.187

4. Bayelsa - biliyan N116.401

5. Lagos - biliyan N115.932

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

A gefe guda, hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta fitar da rahoton yadda aka kasafta kudin Disamba 2020 na kudin wata-wata da ake rarrabbawa daga asusun gwamnatin tarayya (FAAC).

A cewar NBS, FAAC ta raba kudi naira biliyan 601.11 a tsakanin bangarorin uku na gwamnati, wato gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, a watan Disambar 2020 daga kudaden shigar da aka samu a watan Nuwamba 2020.

Legit.ng ta kawo yawan kudin da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka samu da kuma sauran muhimman bayanai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel