FAAC ta rabawa Gwamnatoci Naira Biliyan 639 a matsayin kason Satumba

FAAC ta rabawa Gwamnatoci Naira Biliyan 639 a matsayin kason Satumba

- Gwamnatin Najeriya ta yi magana game da kason da aka yi a watan Satumba

- Biliyan 639.9 aka rabawa gwamnatoci daga asusun FAAC a watan da ya wuce

- Jihohi da kananan hukumomi sun samu Naira biliyan a cikin wadannan kudi

Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda aka yi rabon kudin watan Satumba da ya wuce. Gwamnatocin sun raba Naira biliyan 639.

Bayan kason watan jiya, abin da ya rage a asusun rarar mai ya koma Dala miliyan 72.41. Ma’aikatar kudi ta bayyana wannan a taron FAAC.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar kudi, Aliyu Ahmed, ya ce gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba Biliyan 639.901.

KU KARANTA: Rashin kudi: Ya Jihohi za su yi da albashin ma'aikata da bashi?

Aliyu Ahmed wanda ya jagoranci zaman FAAC da aka yi ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, ya ce an samu Naira biliyan 341 daga kudin-shiga.

Naira biliyan 39.54 daga cikin wannan kudi sun fito ne daga kudin kasar wajen da Najeriya ta samu, an kuma samu Naira biliyan 141.858 daga VAT.

Kudin da su ka shiga asusun FAAC a watan da ya wuce daga sauran albarkatun kasa bayan man fetur sun haura Naira biliyan 70 inji Mista Ahmed.

Kudin shigan da gwamnati ta tatso a watan Satumba watau Naira biliyan 341.501 ya gaza abin da aka samu a watan jiya da kusan Naira biliyan 200.

FAAC ta rabawa Gwamnatoci Naira Biliyan 639 a matsayin kason Satumba
Taron gwamnoni Hoto: NGF: www.nggovernorsforum.org
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya yi daidai da ya soke biyan tallafin man fetur - Sanusi

Haka zalika an samu faduwar VAT, a watan Agusta, gwamnatin tarayya ta samu Biliyan 150.

A cikin wannan makudan kudi, gwamnatin tarayya ta samu N255.748b, sannan jihohi da kananan hukumomi sun tashi da N185.645b da N138.444b.

Binciken da aka yi kwanaki idan za ku tuna, ya nuna jihohin Katsina da Bayelsa su na cikin Jihohin da su ka fi dogara da asusun FAAC a Najeriya.

Idan aka cire abin da ake samu daga tarayya, jihohi da-dama ba za su iya tsayawa da kafafunsu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel