Mutuwa Ta Girgiza APC: Wani Babban Jigon Jihar Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Girgiza APC: Wani Babban Jigon Jihar Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar sanannen dan siyasa a jihar Kano, Alhaji Hamza Darma
  • Barau ya bayyana jimami bisa wannan rashi, yana mai cewa rasuwar Darma babban rashi ne ga daukacin al'ummar Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa manyan jiga-jigai ciki har da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo sun halarci jana'izarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Dattito kuma fitaccen dan siyasa a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Alhaji Hamza Darma ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni daga Kano sun tabbatar da cewa marigayin, wanda jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki, ya rasu yana da shekara 75 a duniya.

Hamza Darma.
Fitaccen dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar ADC, Alhaji Hamza Darma Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Alhaji Hamza Darma ya rasu a Kano

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar dattijon a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yau Juma'a 20 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Tinubu zai kayar da Kwankwaao a Kano a zaben 2027'

Barau ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa, yana mai bayyana cewa rasuwar Alhaji Hamza Darma babban rashi ne ga Kano da ma Najeriya baki daya.

Sanata Barau ya yi ta'aziyya

A sakon da ya fitar a shafinsa, Sanata Barau ya ce:

"Na samu labarin rasuwar Alhaji Hamza Darma, wani dattijo kuma jigo a siyasar Kano, cikin matuƙar alhini. Ya rasu ne a yau, Juma’a.
"Wannan babban rashi ne, ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma da daukacin al’ummar jihar Kano. Ya kasance mutum mai tawali’u, jajircewa da kishin yi wa jama’a hidima, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga bautar Allah Maɗaukaki da kuma walwalar al’ummarsa."

Barau ya jajantawa iyalan Darma

Sanata Barau ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya da addu’o’i ga iyalansa da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano, yana mai addu'ar Sllah Ya gafarta masa kura-kuransa.

"A wannan lokaci na jimami, muna miƙa saƙon ta’aziyya da addu’o’inmu ga iyalansa da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC Salihu Mustapha ya yi watsi da jam'iyyar, ya yi murabus

"Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta masa kurakuransa, Ya jiƙansa, Ya yalwata kabarinsa, Ya kuma sanya shi cikin Jannatul Firdaus."
Barau.
Mataimakin shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin a ofishinsa a Abuja Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Premier Radio ta ruwaito cewa tuni aka gudanar da Jana'izar Marigayi Alhaji Hamza Usman Darma wanda ya rasu a yau Juma'a, 21 ga watan Agusta, 2026.

Jana'izar ta gudana a Masallacin Bulama da ke Kawo kusa da Hotoro, kuma mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo na daga cikin wadanda suka halarta.

Malam Aliyu Ladan ya rasu a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar Malam Aliyu Ladan wanda aka bayyana a matsayin mutumin kirki kuma mai riko da addinin Musulunci.

Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana jimami bayan rasuwar malamin Musulunci, yana cewa sun yi rashin mutum na musamman kuma mai daraja daga Gombe.

Ya bayyana cewa sun yi rashin ɗaya daga cikin mafiya alheri a tsakaninsu, musamman wajen karatun Alƙur’ani da ba da labarai da darussan magabatanmu salihai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262