Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Sauka a Kano don Ta'aziyyar Dattijon APC
- Tawagar Shugaban Bola Ahmed Tinubu ta sauka a Kano bayan rasuwar jigon jam'iyyar APC a jihar, Alhaji Hamza Usman Darma a Kano
- Tawagar ta ƙunshi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da gwamnonin Yobe, Mai Mala Buni, Sokoto Ahmed Lawan da Jigawa Umar Namadi
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe su, sannan ya gode wa Shugaban kasa Tinubu bisa jaje da ta'aziyya da ya aika wa al’ummar jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata babbar tawagar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Hamza Usman Darma, fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon ƙasa a Kano, wanda ya rasu kwanan nan.
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 23 ga watan Agusta, 2026.

Source: Facebook
Sakon da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana manyan mutanen da ke kunshe a cikin tawagar da ta gana da gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Tawagar da Tinubu ya aika Kano
Tawagar ta ƙunshi Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman, Ibrahim Kabir Masari; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; da gwamnonin jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa.
Sanarwar ta kara da cewa tawagar ta kuma miƙa saƙon ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga gwamnatin Kano da al’ummar jihar bisa rasuwar marigayin.

Source: Facebook
A cikin saƙon ta’aziyyar da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya karanta a madadin tawagar, sun jajanta wa iyalan marigayin tare da roƙon Allah Ya jiƙansa,.
Haka kuma tawagar ya bakin gwamnan ta kuma ba iyalansa da sauran waɗanda rasuwarsa ta shafa haƙurin jure wannan babban rashi.
Tawagar APC ta yaba wa marigayi Darma
Tawagar ta bayyana marigayi Hamza Darma a matsayin fitaccen ɗan siyasa da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban Kano da Najeriya, tana mai cewa irin gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.

Kara karanta wannan
Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027
Ta ce rasuwarsa babban rashi ne ga Kano da ƙasar baki ɗaya, tare da isar da saƙon ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga gwamnatin jihar da al’ummar Kano.
Da yake mayar da martani a madadin iyalan marigayin, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajanta wa al’ummar Kano kan rasuwar Alhaji Hamza Darma.
Tinubu ya yi jimamin rasa jigon APC
A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimami da alhinin rasuwar babban jigon APC a jihar Kano, Alhaji Hamza Usman Darma.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana marigayi Hamza Darma a matsayin amintaccen aboki kuma ɗan jam’iyya mai kishin ci gaba tare da motsa jam'iyya yadda ya dace.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansa haƙurin jure rashin kuma Ya shigar da shi Aljannar Firdausi tare da mika ta'aziyya ga mutanen jihar Kano.
Asali: Legit.ng
