Amurka Ta Dauki Mataki a Najeriya da Kasashe kan Mauludin 2026
- Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Babban Ofishin Jakadancinta da ke Legas sun sanar da cewa ba za su bude domin gudanar da ayyuka ba ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026
- Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa ofisoshin za su kasance a rufe ne domin bikin hutun Mauludi, kamar yadda ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya tabbatar
- Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya sanar da hakan ne a ranar 24 ga watan Agusta, 2026, inda duk wadanda za su bukaci wani abu a ofishin su jira zuwa ranar da za su dawo aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Babban Ofishin Jakadancinta da ke Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026, domin bikin hutun Mauludi.
Hakan na zuwa ne yayin da ake sa ran jama'a da dama za su fita jerin gwano a ranar a biranen Najeriya ciki har da Abuja da Legas.

Source: Getty Images
Amurka ta rufe ofishinta
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya sanar da rufe ofisoshin na yini guda ne a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, ta shafinsa na X.
Sakon ya ce:
“Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Babban Ofishin Jakadancinta da ke Legas ba za su bude domin gudanar da ayyuka ba ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026, domin hutun Mauludi.”
Rufe ofisoshin zai shafi dukkan ayyukan ofishin jakadancin da na karamin ofishin da aka tsara gudanarwa a ranar, ciki har da alƙawuran neman biza, ayyukan ofishin jakadanci da sauran ayyukan da suka shafi jama'a a wuraren biyu.
’Yan Najeriya da abin zai shafa
’Yan Najeriya da aka yi wa alƙawari ko kuma suka shirya ziyartar Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ko Babban Ofishin Jakadancinta da ke Legas a ranar 25 ga watan Agusta za su bukaci sake tsara lokacin zuwa.
Ba a bayyana yadda wadanda abin ya shafa za su gudanar da lamarinsu ba, amma an shawarce su da su rika duba hanyoyin sadarwa na hukuma na ofishin jakadancin domin samun bayanai kan yadda za su sake tsara zuwa ofishin.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Ana ba da hutun Mauludi a Najeriya, wanda ake gudanarwa domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) duk shekara.
Hakan ne ya sanya ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke ƙasar su daidaita lokutan ayyukansu da manyan ranakun hutun gwamnati na Najeriya.

Source: Getty Images
A wani sako da ofishin jakdancin Amurka ya wallafa a Facebook ya nuna cewa matakin zai shafi wasu kasashe ba Najeriya kadai ba.
An ba da hutun Mauludi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026, a matsayin ranar hutu domin tunawa da Mauludin Annabi Muhammad (SAW) na bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayya cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma'aikatar, Dr Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma'a.
Tunji-Ojo ya taya Musulmin Najeriya da wadanda ke zaune a kasashen waje murnar wannan rana, tare da kira ga ’yan Najeriya su yi tunani kan dabi'un tausayi, tawali'u da yi wa jama'a hidima.
Asali: Legit.ng
