Akwai Matsala: An Samu Bayanan Sirri kan Wuraren da Yan Bindiga ke Shirin Kai Hare Hare a Najeriya

Akwai Matsala: An Samu Bayanan Sirri kan Wuraren da Yan Bindiga ke Shirin Kai Hare Hare a Najeriya

  • Jami’an tsaro sun kara sanya ido a makarantu, sansanonin horas da matasan NYSC, wuraren ibada da sauran wuraren da ke cikin hadari
  • Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi gargadin yiwuwar hare-haren ’yan ta’adda da za su iya faruwa yayin komawar dalibai makarantu
  • Rundunar ta ce an gano motsin wasu ’yan bindiga daga Katsina ta Kaduna zuwa jihar Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jami’an tsaro sun kara tsaurara matakan sanya ido a makarantu, sansanonin horas da matasan masu yiwa kasa hidima (NYSC), wuraren ibada da sauran wuraren da ke cikin hadari.

Dakarun tsaro sun dauki wannan mataki ne bayan samun bayanan sirri kan shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare a sassan Najeriya.

Disu.
Shugaban rundunar yan sandan Najeriya, IGP Tunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yan sanda sun gano shirin yan bindiga

Punch ta rahoto cewa tun farko, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi gargadi cewa yan bindiga sun shirya wasu hare-hare da ka iya faruwa a lokacin komawar dalibai makarantu a zangon karatu na 2026/2027.

Kara karanta wannan

Abin ba daɗi: Yan bindiga sun mamayi wasu bayin Allah, sun buɗe wa motarsu wuta

A cewar sanarwar bayanan sirrin da Sashen Ayyuka na rundunar ya samu sun nuna “haɗuwar ’yan ta’adda domin yiwuwar kai hare-hare a lokaci guda” kan wuraren ibada, makarantu, sansanonin NYSC da sauran wuraren masu muhimmanci.

An aika sanarwar ga Mataimakan Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da ke kula da shiyyoyi na 1 zuwa 17, rundunonin ’Yan Sanda, sassan yaki da ta’addanci da sauran sassa na musamman, da kuma kwamishinonin ’yan sanda a dukkan jihohin Najeriya

An gano motsin ’yan bindiga

Rundunar ’yan sandan ta ce bayanan sirri sun nuna motsin wasu ’yan bindiga dauke da makamai daga Katsina ta Kaduna zuwa jihar Plateau, kamar yadda Leadership ta kawo.

Sanarwar ta ce:

“Akwai karin taruwar ’yan ta’adda domin yiwuwar kai hare-hare a lokaci guda kan wuraren ibada, makarantu, sansanonin NYSC da sauran wuraren da ke cikin hadari.”

Rundunar ta kuma ce ana zargin wasu jami’an kungiyar ISWAP da masu taimaka masu da bayanai suna sa ido tare da gudanar da bincike kan wuraren da za su iya zama wuraren kai hari.

Kara karanta wannan

Musulmai sun ɗauki mataki mai tsauri da aka gano yan bindiga na shirin kai hari masallatai

’Yan sanda sun bayyana barazanar da ke fuskantar cibiyoyin ilimi a matsayin abin damuwa matuka, inda suka yi gargadin cewa hare-haren na iya faruwa daidai lokacin komawar dalibai makarantu a zangon karatu na 2026/2027.

Wane matakai aka dauka?

Saboda haka, Sashen Ayyuka ya umarci sassan da abin ya shafa da kwamandoji da su kara tsaurara tsaro a makarantu, wuraren ibada, sansanonin NYSC da sauran wuraren da ke cikin hadari.

“Ya kamata dukkan jami’ai su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana tare da kai rahoton mutanen da ake zargi, motoci, zirga-zirga ko wasu abubuwa da ake zargi ta hanyoyin da aka tanada,” in ji sanarwar..

An umarci kwamishinonin ’yan sanda da su kara tsaurara tsaro a kan iyakokin jihohi, hanyoyin shiga da fita da sauran muhimman hanyoyin da za a iya bi domin hana shigar ’yan bindiga dauke da makamai da kuma zirga-zirgarsu.

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sanda ta Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yan sanda da sojoji sun shiga daji

Kun ji cewa rundunar ’yan sandan Kebbi ta ce an kashe ’yan bindiga da dama a dajin Gumki da ke yankin Kangiwa a jihar ta Arewa maso Yamma.

Sojoji da yan sanda ne suka hadu suka kai samame cikin dajin domin fatattakar ’yan bindiga da ’yan kungiyar Lakurawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262