Da Gaske 'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci a Gidan Sanata Yari?

Da Gaske 'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci a Gidan Sanata Yari?

  • Rundunar Sojojin Najeriya ta yi rahotannin cewa an yi garkuwa da wasu malaman addinin Musulunci a gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Abubakar Yari
  • Rundunar ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da wasu mutane yayin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu da ke Karamar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara
  • Sojoji sun ce dakarunsu tare da sauran jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa an yi garkuwa da wasu malaman addinin Musulunci a gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata, Abdul’aziz Abubakar Yari, da ke Karamar Hukumar Talata Mafara ta jihar.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da wasu mutane yayin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu da ke Karamar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Hotunan yadda aka gudanar da jana'izar Bamanga Tukur a Adamawa

Ba a sace malamai a gidan Sanata Yari ba
Sanata Abdulazeez Yari da shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy, @BashFarhan
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, 8 Division/Sector 2, Operation Fansa Yamma, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya fitar ranar Lahadi, 13 ga watan Satumban 2026 a shafin Facebook.

Laftanar Kanal Olaniyi Osoba ya bayyana rahotannin da suka danganta sace mutanen da gidan Yari a matsayin na yaudara da ƙarya.

Osoba ya ce rundunar ta san da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai daban-daban, kuma ta ga ya dace ta fayyace abin da ta bayyana a matsayin bayanin da bai dace da gaskiyar lamarin ba.

Ya jaddada cewa, “ba a yi garkuwa da wani malamin addini a gidan Sanata Yari ba,” yana mai cewa wurin da aka ce sace mutanen ya faru ba daidai ba ne.

Daga ina aka sace mutanen?

A cewar Osoba, bayanan sirrin da sojoji suka samu sun nuna cewa an yi garkuwa da mutanen ne yayin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu a Karamar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

Kara karanta wannan

'Kashe kashe ya yi yawa': An taso gwamna a gaba sai ya bar kujerarsa

Rundunar Sojin ta ce jami’an tsaro na aiki domin gano tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ta ƙara da cewa dakarunta, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da hanyoyin samun bayanan sirri daga al’ummomin yankin, sun ƙara tsaurara ayyukansu a yankin.

Matsalar tsaro ta addabi Zamfara

Wannan lamari ya zo ne yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan Jihar Zamfara, inda miyagun laifuka ke amfani da hanyoyin daji da wuraren da ba su da tsaro wajen yin garkuwa da mutane da sauran hare-hare.

Rundunar Sojin ta buƙaci jama’a su yi haƙuri tare da guje wa yaɗa rahotannin da suka wuce gona da iri ko waɗanda ba a tabbatar da su ba, waɗanda za su iya haifar da fargaba ko kawo cikas ga ayyukan sojojin da ke gudana.

“Ana shawartar jama’a da su yi watsi da rahotannin da aka ƙawata da bayanan da ba a tabbatar da su ba, waɗanda za su iya haifar da fargabar da ba ta da amfani ko kawo cikas ga ayyukan soji na dabarun yaƙi da ke gudana.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Wasu malaman musulunci sun faɗa tarkon yan bindiga a hanyar dawowa daga taron APC

Ya kuma buƙaci mazauna yankin da shugabannin al’umma su kasance cikin taka-tsantsan tare da bai wa hukumomin tsaro bayanai masu inganci, sahihai kuma masu amfani cikin lokaci, waɗanda za su taimaka wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci.

An sace malaman addini a jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar ta ce Hedikwatar 8 Division da Sector 2, Operation Fansan Yamma, na ci gaba da jajircewa wajen kare fararen hula da kuma tunkarar miyagun laifuka da ke aiki a sassan Arewa maso Yamma.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba hukumomin tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Sanata Yari ya yabi Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu nagarta.

Sanata Yari ya ce duka yan takarar da ke ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba su kai shi cancanta da ƙwarewa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng