Yan jihar Kwara sun bukaci ballewa daga Arewa

Yan jihar Kwara sun bukaci ballewa daga Arewa

- Al'ummar Kwara ta gudu sun ce sun gaji da kasancewa cikin Arewacin Najeriya

- Mutanen suna bukatar a hada su da yarbawan Kogi ga yan'uwansu dake kudu maso yamma

- Sun gabatar da bukatansu ga majalisar dokokin tarayya domin sauyawa a kundin tsarin mulki

Al'ummar kudancin jihar Kwara, ta bakin kungiyar dattawan yankin watau Kwara South Consultative Forum (KSCF), sun gabatar da bukatunsu ga kwamitin majalisar dokokin tarayya kan sauye-sauye a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Mutanen suna bukatar a hada su da Yarabawan Kogi da yankin Kudu maso yamma ta hanyar canza iyakokin jihohin.

Sun bukaci a basu nasu kananan hukumomin a sabon jihohin da za'a hadasu.

Sun kara da cewa sauran Yarbawan dake sauran kananan hukumomi biyar na jihar Kwara su dawo cikin sauran sabon yankin domin hadasu da yankin Kudu maso yamma.

DUBA NAN: Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Yan jihar Kwara sun bukaci ballewa daga Arewa
Credit: @NGRSenate
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shin da gaske ne kungiyar malaman jami'a ASUU sun janye daga yajin aiki?

Shugaban kungiyar na kasa, Sir Joseph Aderigbigbe, ya bayyana cewa Yarbawan Kwara na zaune a kananan hukumomi 7 cikin 16 na jihar amma aka hana Yarabawan jihar Kogi zaban inda suke son kasancewa.

A cewarsa, kawai an hadasu da yankin Arewa sabanin abinda kundin majalisar dinkin duniya ta tanada.

"Zamu cigaba da nemawa kanmu da al'ummarmu yanci. Muna son a hada mu da inda ya kamata mu kasance, inda za'a rike girmama juna." Kungiyar tace

Legit ta ruwaito muku a baya cewa kungiyar Yarabawa (Okun) mazauna jihar Kogi, sun ce suna da bukatar tattara ya nasu-ya nasu su bar shiyyar Arewa, bayan shafe tsawon shekaru suna rayuwa a ciki.

Sun bayyana cewa a baya, sun zabi barin 'yan uwansu da mahaifarsu a jihohin Ondo, Ekiti da Kwara, saboda dogaro da kai, yanzu kuma akwai bukatar su koma cikin 'yan uwansu.

Sun yi bayanin hakan ne a karkashin kungiyar OLA, a ranar Lahadi, bayan ganawarsu da Aiyetoro-Gbede, a karamar hukumar Ijumu, jihar Kogi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng