Hadimin Atiku Ya Kuncowa Tinubu Kura kan Batun Maido Tallafin Man Fetur
- Mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya soki cire tallafin man fetur
- Okonkwo ya ce tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki sun rage ƙarfin Naira, yana mai cewa albashin N70,000 bai inganta rayuwar talakawa ba
- Ya bayyana cewa tsarin Atiku ba wai komawa ga tsohon tsarin tallafin mai ba ne, illa rage farashin man fetur ta hanyar tallafa wa matatun mai na cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya soki matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.
Okonkwo ya ce cire tallafin bai kawo sauƙin rayuwa ga 'yan Najeriya ba, yana mai cewa tsadar man fetur, hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar Naira sun ƙara tsananta wahalhalun jama'a.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television, inda ya kare sabon tsarin da Atiku ya ce zai bullo da shi domin rage farashin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Magana kan albashin N70,000
Okonkwo ya ce farashin litar man fetur ya kai kusan N1,300, yana mai bayanin cewa mai mota mai tankin lita 100 zai bukaci kusan N130,000 domin cike tankinsa.
Ya ce wannan adadi ya zarce mafi karancin albashin na N70,000, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ƙarfin sayen kayan masarufi na ma'aikata ya ragu.
Ya ce:
"N130,000 kusan ya ninka mafi karancin albashi sau biyu. Ma'ana N70,000 da ake biya mutum ba zai iya cika rabin tankin motarsa ba, balle ya rage wani abu domin haya, abinci ko magani."
Batun darajar Naira a Najeriya
Jigon jam'iyyar ADC ya kuma zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da raunana darajar Naira da kuma kara matsalolin tattalin arziki.
Okonkwo ya kwatanta tsohon albashin mafi ƙaranci na N30,000 da na yanzu N70,000, yana mai cewa duk da karin albashin, ƙarfin sayen kayayyaki bai inganta yadda ake tsammani ba.
Ya ce a lokacin da ake biyan N30,000, kudin na da kimar kusan $60, yayin da N70,000 a halin yanzu yake da kimar $50 bisa yadda ya bayyana.
Okonkwo ya ce:
"Naira ta zama maras amfani a gwamnatin Tinubu. Wannan gwamnati tana lalata kudinmu da tattalin arzikinmu."
Tsarin tallafin mai na Atiku
Okonkwo ya bayyana cewa Atiku ba ya shirin dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur da ake amfani da shi kafin cire tallafin a 2023.
Ya ce sabon tsarin da Atiku yake gabatarwa zai mayar da hankali ne kan rage kudin samar da man fetur, musamman ta hanyar samar da danyen mai ga matatun mai na cikin gida cikin sauƙi.
A cewarsa, kasancewar Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur, bai kamata jama'a su riƙa sayen man da aka tace cikin gida da tsada ba.

Source: Getty Images
APC ta caccaki Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya soki Atiku Abubakar kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Yilwatda ya bayyana sauya matsayar Atiku daga goyon bayan cire tallafin mai zuwa alkawarin dawo da shi a matsayin wani abu da ya danganta da neman mulki.
Ya ce dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur na iya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin matsala, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da kare matakin cire tallafin a matsayin wani muhimmin sauyi na tattalin arziki.
Asali: Legit.ng


