Kasar Rasha Ta Dauki Zafi, Ta Shirya Harba Makamin Nukiliya kan Kasa 1 Tak a Duniya
- Kasar Rasha ta yi barazanar harba makaman nukiliya kan Lithuania idan ƙasar ta amince a ajiye makaman ƙawayenta na NATO a yankinta
- An ruwaito cewa Lithuania na shirin ɗage dokar kundin tsarin mulkinta da ta hana ajiye makaman nukiliya a ƙasar
- Shugaban Lithuania ya ce ƙasar na son zama cikakkiyar ɓangare na tsarin kare kai da makaman nukiliya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Russia - Kasar Rasha ta bayyana cewa za ta ɗana makaminta na nukiliya tare da shirya kai hari da shi zuwa kasar Lithuania.
Rasha ta ce za ta zauna cikin shirin nufar Lithuania da makaman nukiliyarta idan ƙasar ta karɓi wasu makaman nukiliya daga tarin makaman ƙawayenta na kungiyar NATO a yankinta.

Source: Getty Images
Wane laifin da Lithuania ta yiwa Rasha?
Vanguard ta rahoto cewa Lithuania na shirin ɗage dokar kundin tsarin mulkinta da ta hana ajiye makaman nukiliya a ƙasar, wani mataki da take ɗauka domin ƙarfafa tsaronta yayin da Rasha ke ci gaba da kai farmaki kan Ukraine.
A halin yanzu, matakin na gaban majalisar dokokin ƙasar, inda yake buƙatar samun rinjayen kashi biyu bisa uku domin amincewa.
Shugaban ƙasar da manyan jam’iyyun siyasa na goyon bayansa, kuma ana iya fara aiwatar da shi a wannan hunturu.
Rasha ta yi baranzar kai hari
Da yake martani kan haka, kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce matakin zai kasance “babban sauyi sosai ta fuskar ƙara tsananta rikici” yayin da yake magana da gidan talabijin na ƙasar Rasha kan shirin.
“Idan akwai makaman nukiliya a yankin da ka iya tunkariwa kanmu, to yankin wannan ƙasa shi ma zai shiga cikin jerin wuraren da makaman nukiliyar mu za su nufa,” in ji shi.
Lithuania na ƙarfafa tsaronta
Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ya sanar da shirin a watan Yuli, yana mai cewa ƙasarsa na son zama “cikakkiyar ɓangare na wannan tsarin kare kai da makaman nukiliya”.
Sai dai alama wannan mataki bai yi wa kasar Rasha dadi ba, kuma ta yi barazanar shirya kai hari kasar Lithuania da makamin nukiliya matukar ba ta sauya tunani ba.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya 'tsorata', ya fara laluben lokacin dakatar da yaki da ƙasar musulunci ta Iran

Source: Getty Images
Wannan barazana dai na zuwa ne yayin da Rsha ke ci gaba da musayar wuta da kasar Ukrakne, yakim da ya shafe tsawon lokaci ana yinsa kuma har yanzu ba a cimma matsayaba.
Yakin dai ya fara ne sakamakon matakin da Ukraine ta dauka na shiga hadakr kungiyar tsaro ta NATO, lamarin da gwamnatin Rasha ta yi watsi da shi.
Amurka ta tura wakili zuwa Rasha
A wani labarin, kun ji cewa daraktan hukumar CIA ta Amurka, John Ratcliffe, ya kai wata ziyarar sirri zuwa Moscow inda aka ce ya gargadi Rasha kan kai hari ga kasashen NATO.
Rahotanni sun nuna cewa Ratcliffe ya kai ziyarar ce a farkon wannan mako, yayin da Amurka ke nuna damuwa kan yiwuwar Rasha ta kara fadada rikicin da take yi da Ukraine zuwa wasu kasashen Turai.
Haka kuma akwai fargabar cewa Rasha na iya kai hare-haren intanet kan wasu kasashen gabashin Turai, yayin da yakin Ukraine ya kasa kai ga wata babbar nasara ga bangarorin da ke fafatawa.
Asali: Legit.ng
