Akwai Matsala: Shugaban Amurka Ya Jero Wasu Mutane da Za Su Shiga 'Wutar Jahannama'
- Donald Trump ya gargadi magoya bayansa na jam’iyyar Republican cewa za su “je wutar jahannama” idan ba su fito sun yi zaɓe a watan Nuwamba ba
- Shugaban Amurkan ya bukaci magoya bayansa su tattaro ’yan uwa da abokai domin kada su bari jam’iyyar Democrat ta samu nasara
- Trump ya ce nasarar Democrat a zaɓen Nuwamba za ta iya dawo da hannun agogo baya baya kan nasarorin gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gargadi magoya bayansa na Jam’iyyar Republican cewa za su “shiga wuta” idan ba su fito sun yi zaɓe a zaɓen tsakiyar wa’adin na watan Nuwamba ba.
Trump ya yi wannan gargadin ne a daren Alhamis yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a taron Jam’iyyar Republican da aka gudanar a Dallas, Texas.

Source: Getty Images
Trump ya gargadi magoya bayansa
Daily Trust ta ruwaito cewa Trump ya bukace su da su ƙara ƙoƙarin wayar da kan masu zaɓe gabanin zaɓen Majalisar Dokokin ƙasar.
Trump ya fada wa mahalarta taron cewa:
“Kun san abin da zai faru idan ba ku yi zaɓe ba? Za ku shiga wutar jahannama."
Ya kuma bukaci magoya bayansa da su “yi yaƙi da ƙarfi” yayin da yake zargin ’yan Democrat da aikata almundahanar zaɓe a faɗin ƙasar.
Shugaba Trump ya yaba wa gwamnatinsa
Trump ya yi amfani da jawabin wajen bayyana abubuwan da ya kira nasarorin gwamnatinsa, yana mai cewa ya sauya abin da ya kira “zamanin duhu” zuwa “zamanin zinariya” ga Amurka.
A cewarsa, gwamnatinsa ta cika dukkan alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana ambaton yadda kasuwar hannayen jari ke tafiya, raguwar farashin magunguna, ƙarin kashe kuɗi kan sojoji da kuma raguwar shigowar baƙi ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya 'tsorata', ya fara laluben lokacin dakatar da yaki da ƙasar musulunci ta Iran
“A cikin watanni 19, na cika kowane irin alkawari da na yi,” in ji Trump.
Nsarorin gwamnatin Trump a Amurka
Ya kuma yi nuni da wasu matakan da Majalisar Dokoki ta ɗauka a baya-bayan nan na rage haraji kan kuɗin aiki, kuɗin kyauta da kuma wasu fa’idodin Social Security, yana mai cewa hakan na daga cikin hujjojin ci gaban gwamnatinsa.
Trump ya gargadi magoya bayansa cewa nasarar ’yan Democrat a zaɓen Nuwamba za ta sauya abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, cewsr rahoton Asian News.

Source: Getty Images
Ya yi zargin cewa ’yan Democrat za su nemi ƙwace dukiyar jama’a, raunana masana’antar mai da iskar gas ta Texas, tare da barin masu aikata laifuffuka su ci karensu babu babbaka.
Trump zai dakatar da yakin Iran
Kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Iran zai ƙare nan take bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na Nuwamba.
Kalaman shugaban Amurkan sun zo ne a lokacin da rikicin ya shiga wani yanayi mai tsanani, inda hare-hare suka shafi jiragen dakon mai da na kasuwanci a kusa da mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng
