Mutumin da Ya Guntule Yatsar Shi kan Naira Miliyan 80 Ya Yi Biyu Babu a Kano
- Wani matashi mai suna Yusuf Mahmud ya yanke ɗan yatsansa na hannu domin samun tukuicin naira miliyan 80 a Kano
- Wanda ya sa shi aikin, Ishaka Isa, ya bayyana cewa kashin damtsen hannu ake buƙata maimakon ɗan yatsa bayan ya gaza biyan ƙudin
- Sauran mutanen da aka kama yanzu haka suna tsare a hannun jami'an 'yan sanda a shalkwatar Bompai da ke jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana labarin wani matashi mai suna Yusuf Mahmud wanda ya yanke ɗan yatsan hannunsa domin samun Naira miliyan 80.
Matashin ya shiga halin biyu babu bayan ya rasa ɗan yatsansa sannan kuma bai sami ƙudin da aka yi masa alƙawari ba, inda a yanzu yake kulle a shalkwatar 'yan sanda da ke Bompai.

Source: Facebook
Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa matashin ya fara zuwa ofishin 'yan sanda na Rano domin shigar da ƙorafi a kan wanda ya sa shi aikin bayan an hana shi ƙudinsa.
Yadda aka yanke yatsa
A bayanin da ya yi wa 'yan sanda, Mahmud ya ce wani mutum ne ya buƙaci ya nemo masa ɗan yatsan mutum mai rai a kan alƙawarin ba shi naira miliyan 80, kuma da ya rasa wanda zai yanke wa, sai ya yanke nasa na hannu da wuka ya mika masa.
Sai dai kuma, bayan gudanar da bincike, 'yan sandan sun samu nasarar kama wanda ake zargi da sa shi aikin mai suna Ishaka Isa, wanda ya bayyana daban da abin da Mahmud ya faɗa.
Kiyawa ya rubuta cewa:
"An kamo wanda yace a kawo masa yatsan mutum. Sai dai kuma fa, shi ya ce, ba yatsan mutum ya ce su kawo ba, kashin damtsen hannu a ke bukata, kuma na mutum mai rai."

Source: Original
Wanda ya sa aka yanke yatsar
Ishaka Isa ya tabbatar da cewa shi ma tura shi aka yi kuma an ba shi umarnin ne daga sama, amma saboda ba zai iya yanke nasa hannun ba, shi ya sa ya mika aikin ga Yusuf Mahmud.
A yanzu haka jami'an 'yan sanda sun sami nasarar tsoto ɗan yatsan da aka yanke, ko da yake ƙashin kawai ya rage a jikinsa.
"Yanzu haka, an samo dan yatsan da aka yanke, amma kashi ne kawai ya rage. Ina likitoci? Shin dan yatsan zai iya komawa kuwa?"
An kashe Danshagamu a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mai sharhi kan al'amuran siyasa, Ibrahim Khalil Danshagamu.
Kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba ta bayyana, lamarin ya faru ne a unguidar Gaida da ke karamar hukumar Kumbotso a daren Litinin misalin karfe 11:30.
Tsagerun sun kutsa gidan mamacin ne tare da kai masa hari da abubuwa masu kaifi, inda aka gaggauta kaita shi asibitin kwararru na Murtala Mohammed amma likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Asali: Legit.ng


