Abin Boye Ya Fito: An Gano Bashi Ya Yi wa Amurka Katutu yayin da Ta ke Yaki da Iran
- Bashin gwamnatin Amurka ya haura dala tiriliyan 40 a karon farko, lamarin da ya jawo sabon fargaba kan yiwuwar matsalar tattalin arziki
- Rahoton Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ya nuna bashin ya ninka fiye da sau biyu tun bayan da Donald Trump ya fara zama shugaban ƙasa a 2017
- Wasu masana sun yi gargadin cewa Amurka na iya fuskantar matsalar bashi idan gwamnati ba ta ƙara haraji ko rage kashe kuɗi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Jimillar bashin gwamnatin Amurka ya haura dala tiriliyan 40 a karon farko, yayin da masana ke ƙara gargadin cewa ƙasar na iya fuskantar babbar matsalar kuɗi.
Bayanan Ma'aikatar Baitulmalin Amurka da aka fitar ranar Laraba sun nuna cewa jimillar bashin da ake bin ƙasar ya kai dala tiriliyan 40.047 a ranar Talata.

Source: Getty Images
Reuters ta rahoto cewa bashin ya haɗa da dala tiriliyan 32.266 na takardun bashin gwamnati da jama'a da masu zuba jari ke riƙewa, da kuma dala tiriliyan 7.782 na bashin da hukumomin gwamnatin ƙasar ke tsakaninsu.
Bashin Amurka ya ninku
Rahoton da NBC ta wallafa ya nuna cewa jimillar bashin gwamnatin Amurka yanzu ta ninka fiye da sau biyu cikin ƙasa da shekaru 10.
Lokacin da Donald Trump ya fara rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka a watan Janairun 2017, jimillar bashin ƙasar ta kai kusan dala tiriliyan 19.95.
Kimanin kashi ɗaya bisa uku na ƙaruwar bashin ya faru ne a lokacin da gwamnatocin Trump da tsohon shugaban ƙasa Joe Biden suka karɓi kuɗi masu yawa domin ɗaukar nauyin matakan yaƙi da annobar COVID-19.
Sauran ƙaruwar bashin kuma na da alaƙa da manufofin haraji da kashe kuɗaɗe na gwamnatocin biyu, tare da matsalar rashin daidaito tsakanin kuɗin shiga da kashe kuɗin gwamnati da aka daɗe ana fuskanta.

Kara karanta wannan
Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Gargadi kan matsalar bashi
Kungiyoyin da ke sa ido kan kasafin kuɗin Amurka sun yi gargadin cewa ana iya fuskantar cikakkiyar matsalar bashi idan 'yan majalisa ba su ɗauki matakan gyara ba.
Maya MacGuineas, wata shugabar kungiyar kasafin kudi, ta ce bashin dala tiriliyan 40 ba abin wasa ba ne a harkar mulki.
Ta ce yawan karɓar bashi na iya ƙara hauhawar farashi, rage kuɗin da za a iya kashewa a wasu muhimman fannoni, tare da jefa ƙasar cikin haɗari yayin aukuwar matsaloli a cikin gida ko rikice-rikice a ƙasashen waje.

Source: Getty Images
MacGuineas ta ce bashin Amurka ya kai dala tiriliyan 40 ne cikin ƙasa da watanni biyar bayan ya kai dala tiriliyan 39.
Trump ya ƙara matsawa Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ƙara tsaurara matakan tattalin arziki kan Iran, yayin da yaƙin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke gab da shiga wata na shida.
Trump ya bayyana cewa zai ƙaddamar da abin da ya kira “mafi tsananin matakin tattalin arziki da aka taɓa ɗauka kan wata ƙasa”, yana mai cewa manufar ita ce ƙara ware Iran.
Ya kuma yi barazanar ɗaukar tsauraran matakan tattalin arziki kan duk wata ƙasa da za ta bari cibiyoyin kuɗinta, kamfanoninta, filayen jiragen sama ko hukumominta su tallafa wa Iran.
Asali: Legit.ng

