An Birne Ƴan Uwa 11 da Wasu Mutum 41 bayan Kifewar Kwale Kwale a Sokoto

An Birne Ƴan Uwa 11 da Wasu Mutum 41 bayan Kifewar Kwale Kwale a Sokoto

  • An birne gawarwaki 52 bayan wani kwale-kwale da ke dauke da manoma da ma’aikata ya kife a Gorau, karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
  • Shaidu sun ce fiye da mutane 70 ne ke cikin kwale-kealen a lokacin da iftila'in ya faru, a ciki har da yara da dama, amma mafi yawansu mata
  • Wani dan majalisar dokokin jihar Sokoto ya alakanta hatsarin da cunkoson mutane a cikin kwale-kwalen tare da mika ta'aziyyarsa kan hadarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Akalla mutane 52 ne aka birne bayan wani kwale-kwale ya kife a garin Gorau da ke karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.

Gawarwakin da aka binne sun hada da na ’yan gida daya 11 da suka rasa rayukansu a hatsarin da ya yi matukar tayar da hankulan jama'a.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Jirgin ruwa dauke da mutane fiye da 70 ya kife a Sokoto

Mutum 52 aka gano gawarwakinsu a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto inda aka samu hadarin kwale-kwale Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta kawo labarin cewa kwale-kwalen na dauke da manoma da ma’aikata da ke kan hanyarsu zuwa gonakin shinkafa, inda ya kife da kusan 8.30 na safiyar Laraba 19 ga watan Agusta, 2026 yayin da yake tsallaka wani hanyar ruwa.

An shiga alhini a jihar Sokoto

Trust Radio ta kawo labarin cewa rahotanni sun ce sama da mutane 70 ne ke cikin kwale-kwalen, a ciki har da yara da dama, wadanda mafi yawansu ’yan mata ne.

Shugaban NEMA a jihar Sokoto, Alhaji Tukur Abubakar, ya ce hukumar ba ta kai ga tantance ainihin adadin mutanen da suka mutu ba.

“Za mu gana da jami’an karamar hukumar domin sanin ainihin adadin wadanda abin ya shafa."
Ana ci gaba da aikin ceto a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Shi ma kakakin SEMA, Abdullahi Ghani, ya ce jami’ai na wurin da hatsarin ya faru domin tantance halin da ake ciki da kuma gano ainihin adadin mutanen da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Yadda walkiya ta fado kan mata mai ciki ta mutu har lahira a Bauchi

“Yanzu haka dukkan jami’an da abin ya shafa suna wurin suna tantance lamarin, suna kokarin gano ainihin adadin mutanen da abin ya shafa. Har yanzu babu bayanan hukum."

Ana aikin ceto a jihar Sokoto

A lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto, inda masu nutso aga yankin da mazauna garin ke ci gaba da binciken ruwan domin gano wadanda har yanzu ba a same su ba.

Hakimin garin Gorau, Malam Aliyu Na-Batsami, wanda ya tsira daga hatsarin, ya ce kwalejin na dauke da sama da fasinjoji 70 lokacin da ta kife a tsakiyar hanyar ruwan.

Ya ce:

“Fiye da mutane 70 ne muke cikin kwalejin. Mafi yawancinmu manoma ne da ke zuwa gonaki domin aiki. Haka kuma akwai yara a cikinmu, mafi yawansu ’yan mata ne."

Na-Batsami ya ce bayan kwale-kwalen ya kife, ya yi ta kokarin kada ya nutse kafin ya kama wani buhu da ya taso saman ruwa.

“Da ikon Allah, wasu mutane da suka shiga ruwan daga baya sun ceto ni."

Kwale-kwale ya nutse a Sokoto

A baya, kun ji cewa ana tunanin akalla mutum 40 sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma ya kife a Gorau, jihar Sokoto a kasar nan.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da 'yan yawon bude ido ya rikito, rayuka sun salwanta

Yawancin mutanen da ke cikin kwale-kwalen yara ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15 da haihuwa a duniya, lamarin da ya kara jefa jama'a a cikin tashin hankal.

Rahotanni sun bayyana cewa da farko an samu nasarar ceto mutum shida ciki har da dagacin ​ƙauyen, yayin da ake ci gaba da aikin neman waɗanda suka nutse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng